Mawakin Najeriya Davido yace ba zai yi SAK a zaben 2019 ba

Mawakin Najeriya Davido yace ba zai yi SAK a zaben 2019 ba

- Gawurtaccen Mawakin nan Davido ya bayyana wadanda zai zaba a Najeriya

- Mawakin yace ba zai takaita kan sa da wata Jam’iyya guda rak a zaben ba

Mawakin Najeriya Davido yace ba zai yi SAK a zaben 2019 ba

Babban Mawaki Davido yace zai zabi Atiku a 2019
Source: Instagram

Mun ji labari cewa babban Mawakin nan wanda yake tashe watau Davido ya sako bakin sa cikin zaben da za ayi kwanan nan a Najeriya. Mawakin ya bayyana jerin ‘yan takarar da zai dangwalawa a babban zaben 2019 na bana.

Fitaccen Mawakin yake cewa a zaben shugaban kasa zai zabi Atiku Abubakar ne, yayin da ya kuma ce idan aka dawo gida, zai zabi Dapo Abiodun na jam’iyyar APC mai mukki ne a matsayin ‘dan takarar gwamnan jihar Ogun.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai yayi magana game da alakar sa da Kiristoci

A zaben na 2019, Davido yace kuri’ar sa ta ‘dan majalisar dokoki ta na wajen Shinna Peller. Mawakin wanda yayi fice yace akwai kuma wasu ‘yan takarar da ke karkashin jam’iyyar adawa ta AAC da yake tare da su a zaben 2019.

Har wa yau, Mawakin ya kuma yi karin haske in da yace yana cikin masu marawa ‘dan uwan sa Banky Wellington baya a takarar da yake yi. Banky W wanda ya shahara a waka yana neman takara ne a karkashin jam’iyyar MDP.

Kwanakin baya dai Davido ya marawa Baffan sa da ya fito takarar gwamna a jihar Osun watau Sanata Ademola Adeleke baya a karkashin jam’iyyar PDP. APC mai mulki ce dai ta yi nasara a zaben a lokacin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel