Ke duniya: Wani yaro mai shekaru 13 ya yi wa mahaifiyar sa yankan rago

Ke duniya: Wani yaro mai shekaru 13 ya yi wa mahaifiyar sa yankan rago

Wani yaro, Ifesinachi Ugwueze, mai shekaru 13 ya yiwa mahaifiyar sa, Beatrice Ugwueze, yankan rago a garin Isiagu Ibakwa da ke karamar karamar hukumar Igboeze ta kudu a jihar Enugu.

Lamarin ya faru ne a ranar juma’a yayin da Ifesinachi da mahifiyar sa ke gida su biyu kacal.

Majiyar mu ta shaida ma na cewar yaron ya yi amfani da adda wajen datss kan mahaifiyar ta sa da ke zaman zawarci a yain da malkade da dutsen nika na gargajiya.

Ihu da gurnanin marigayiyar ne ya jawo hankalin makobta har ta kai ga sun bi yaron a lokacin da ya ke kokarin guduwa.

Ke duniya: Wani yaro mai shekaru 13 ya yi wa mahaifiyar sa yankan rago
'Yan sandan Najeriya
Asali: Depositphotos

Wani shaidar gani da ido ya ce Ifesinachi ya sassara wuyan mahaifyar ta sa kafin ya kai ga datse kan ta daga gangar jikin ta.

DUBA WANNAN: Biyu babu: Miji ya kashe kan sa bayan ya kwara wa matar sa ruwan guba

Sai dai fusatattun matasan da su ka yi nasarar kama yaron sun tilasta ma sa shan jinin da ke bulbulowa daga wuyan mahaifiyar sa kafin daga bisani su hallaka shi da duka kafin isowar jami’an rundunar ‘yan sanda.

Da ya ke tabbatar da afkuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Enugu, Ebere Amaraizu, y ace, “wani abun takaici ya faru da misalign karfe 1:30 na rana a garin Isiagu da ke karamar hukumar Igbo-Eze ta Kudu a jihar Enugu in da wani yaro mai suna Ifesinachi Ukwueze ya yi amfani da adda wajen hallaka mahaifiyar sa, Beatrice Ukwueze, bias sabanin da ya zuwa yanzu ba mu gano ba.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel