Leah Sharibu na nan da ran ta - Lai Mohammed

Leah Sharibu na nan da ran ta - Lai Mohammed

Ministan labarai da al'adu na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya yi karin haske dangane da mutuwar Leah Sharibu, dalibar nan ta makarantar garin Dapchi da kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ke ci gaba da garkuwa da ita.

Alhaji Lai Mohammed, ya ce ci gaba da yaduwar mutuwar Leah a hannun mayakan Boko Haram ta hanyar kafofi da zaurukan sada zumunta, zantuka na shaci fadi da ba su da wata madogara ko kamshi na gaskiya.

Ministan Labarai da Al'adu - Lai Mohammed
Ministan Labarai da Al'adu - Lai Mohammed
Asali: Twitter

Da yake ci gaba da jaddada rashin sahihanci wannan labari, Ministan yayin ganawar sa da manema labarai a yau Lahadi cikin birnin Ilorin na jihar Kwara, ya ce jita-jita ce kurum da ta watsu domin kawo rudani yayin da babban zaben kasa ke daf da gudana.

Ministan na al'adu ya ce 'yan adawa ke da hannu cikin wannan aika-aika ta kagar zance da ba ya da wani asali ko tushe na gaskiya mai cike da babbar manufa ta dakusar da nagartar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin da babban zabe ya karato.

Ya ke cewa, wannan wata sabuwar kitimurmura ce da 'yan adawa suka ara kuma suka yafa da manufa ta muzantawa gwamnatin shugaban kasa Buhari sakamakon yadda suka gaza samun ta da wani nakasu.

KARANTA KUMA: Jihohi 15 da za su rinjayar da sakamakon zaben 2019

Ya ci gaba da cewa, tsantsar adawar abokanan hamayya duba da mashuharanci gami da soyayyar al'ummar kasar nan akan Buhari, ya sanya suke fafutikar dakusar da nagartar sa da shafa masa bakin fenti yayin da babban zabe ya rage kwanaki kalilan.

Dangane da taron yakin neman zaben kujerar shugaban kasa da za a gudanar cikin birnin Ilorin na jihar Kwara a gobe Litinin, Ministan ya ce jam'iyyar APC ta riga da shimfida dukkanin wasu tsare-tsare da za su tabbatar da nasarar shugaban kasa Buhari a babban zabe na mako mai zuwa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel