Jihohi 15 da za su rinjayar da sakamakon zaben 2019

Jihohi 15 da za su rinjayar da sakamakon zaben 2019

Ko shakka ba bu al'ummar Najeriya a ranar 16 ga watan Fabrairu, za su yi tururuwa wajen kada kuri'u domin zaben shugaban kasa da zai ci gaba da riko gami da kula da akalar jagoranci kasar nan tsawon shekaru hudu maso gabatowa.

Cikin jerin sunayen 'yan takarar kujerar shugaban kasa 72 da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta tantance, shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC da kuma Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP sun kasance mafi shahara wajen hankoron jagorancin kasar nan.

Alkalumma sun yi hasashen cewa, takarar kujerar shugaban kasa za ta gudana ne tsakanin manyan jam'iyyun biyu na PDP da APC, inda a halin yanzu Atiku da shugaba Buhari ke ci gaba da samun goyon baya na sauran jam'iyyu da za su yi riko da su a matsayi 'yan takara yayin zabe.

Jihohi 15 da za su rinjayar da sakamakon zaben 2019

Jihohi 15 da za su rinjayar da sakamakon zaben 2019 tsakanin Buhari da Atiku
Source: UGC

Binciken da manema labarai na jaridar The Punch suka gudanar kan yadda siyasar jihohi 36 na Najeriya ke gudana ya bayyana cewa, shugaba Buhari na tabbacin samun nasarar cikin jihohi 11 yayin da Atiku ke da ikon mallake jihohi 10 a babban zaben.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, akwai jihohi 15 da za a fafata bakin gumurzu na neman samun nasara tsakanin Atiku da Buhari sakamakon yadda za su yi tasiri wajen rinjayar da sakamakon zaben kasar nan.

Kiyasi da hasashe na alkalumma sun tabbatar da cewa, duk wanda ya samu babban kaso na adadin kuri'un al'umma cikin jihohin 15, ba bu shakka zai zamto zakara ta lashe babban zabe da za a gudanar nan da kwanaki 6 kacal.

KARANTA KUMA: 2019: Atiku ya shahara, sai dai nasara ta na ga Buhari - Eurasia Group

Duba da yadda siyasar jihohin ta kasance bisa ga la'aakri da bambance-bambance na ra'ayi da akida, samun wurin zama da magoya baya tsakanin Buhari da Atiku na da tasirin gaske dangane da yadda salon yakokin su zai gudana cikin jihohin.

Jerin jihohin da za su rinjayar da nasara tsakanin Buhari da kuma Atiku sun hadar da; Kaduna, Neja, Kwara, Filato, Kogi, Benuwe, Adamawa, Ondo, Oyo, Osun, Edo, Akwa Ibom, Anambra, Gombe, da kuma babban birnin tarayya na Abuja.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel