Sultan da sarakunan Arewa 20 sun bude katafaren masallacin Borno da akayi shekaru 32 ana gininsa

Sultan da sarakunan Arewa 20 sun bude katafaren masallacin Borno da akayi shekaru 32 ana gininsa

A ranar Juma'a 8 ga watan Fabrairu ne Sultan na Sokoto, Muhammad Abubakar na III na jagoranci sarakunan Arewa 20 a wurin taron kaddamar da babban masallacin garin Borno.

An kafa tuballin ginin masallacin ne shekaru 32 da suka gabata kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sultan din tare da Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi da wasu sarakuna daga arewacin Najeriya ne suka hallarci taron bude masallacin.

Masallacin da ke kusa da fadan Shehun Borno an fara ginin sa ne a 1986 bayan an rushe masallacin da ke wurin.

Sultan da Sarakunan Arewa 20 sun kaddamar da babban masallacin Borno da akayi shekaru 32 ana gininsa
Sultan da Sarakunan Arewa 20 sun kaddamar da babban masallacin Borno da akayi shekaru 32 ana gininsa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kamfen: Taron Atiku a jihar Borno ya bayar da mamaki, hotuna

An kiyasta kudin ginin masallacin mai daukar mutane 10,000 ne a kan zunzurutun kudi Naira Miliyan 800.

Sai dai saboda rashin isasun kudi, an dakatar da aikin ginin ne yayin da aka kammala kashi 65 cikin 100 na aikin.

Bayan ya dare kan kujerar mulki, Shehun Borno na 20, Abubakar El-Kanemi ne ya fara neman tallafi daga al'umma domin ganin an kammala ginin masallacin.

An cigaba da aikin masallacin ne a 2011 yayin da wani fitaccen dan siyasa a jihar Borno kuma dan takarar kujerar gwamna sau biyu, Kashim Imam ya bayar da tallafin kudi Naira Miliyan 200 domin cigaba da aikin.

Daga bisani kuma gwamnatin jihar Borno ta dauki nauyin cigaba da aikin har zuwa bara da aka karasa aikin masallacin.

A jawabin da ya yi wurin bude masallacin, Shehun Borno ya ce ya na alfaharin cewa a zamaninsa ne aka kammala ginin masallacin.

Ya mika godiyarsa ga gwamnan jihar, Kashim Shettima saboda irin babbar gudunmawar da ya bayar.

Ya ce, "wannan ba irin masallacin da aka saba ginawa bane; domin cibiya ne na binciken ilimin addinin musulunci, haka ya dace a rika tsara masallatan mu; wurin ibada da kuma cibiyar ilimi."

Da farko, kwamishinan harkokin addini na jihar, Mustafa Fannarambe ya ce an samar da ababen zamani a masallacin wanda suka hada da, dakin taro, dakin karatu, transiforma mai karfin 500kva, janareta mai karfin 200kva, manyan tankunan ruwa takwas, gini da zai dauki mutane 10,000 da kuma harabar masallaci da zai dauki mutane 5,000."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel