Kamfen: Hotunan ziyarar Atiku jihar Cross Rivers

Kamfen: Hotunan ziyarar Atiku jihar Cross Rivers

A ranar Juma'a 8 ga watan Fabrairun 2019 ne tawagar yakin neman zaben dan takarar shugabancin kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar ta isa jihar Cross Rivers da ke yankin Kudu maso Kudancin Najeriya.

Atiku ya yi alkawarin hadin gwiwa da Gwamna Ben Ayade na jihar domin gina tashan jiragen ruwa na Bakassi da kuma titi mai tsawon kilomita 164 a jihar.

Atiku ya yi wannan alkawarin ne a garin Calabar yayin da ya ke kaddamar da kamfen dinsa na takarar shugabancin kasar Najeriya.

"Nayi maka alkawarin cewa za muyi hadin gwiwa da gwamna wurin samar da kayayakin more rayuwa a jihar.

"Zan kuma yi hadin gwiwa da shi a fanin Ilimi saboda ilimi ne ginshikin cigaban kowacce al'umma," inji shi.

Atiku ya shawarci mutanen jihar su jefa masu kuri'a, su kuma kare kuri'un su tare da tabbatar da cewa an kirka kuri'un.

Ga hotunan yadda kamfen din ta kasance a kasa:

Kamfen: Hotunan ziyarar Atiku jihar Cross Rivers

Atiku Abubakar, Bukola Saraki, Uche Secondus da sauran jiga-jigan jam'iyyar PDP a kan mimbarin kamfen a jihar Cross Rivers
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kamfen din Atiku a Benue: Filin wasa na Aper Aku ya cika ya batse, hotuna

Kamfen: Hotunan ziyarar Atiku jihar Cross Rivers

Dubban magoya bayan Atiku Abubakar da jam'iyyar PDP da suka fito nuna kaunarsu gareshi yayin da ya ziyarci jihar domin kaddamar da yakin neman zabe
Source: Twitter

Kamfen: Hotunan ziyarar Atiku jihar Cross Rivers

Mutanen jihar Cross Rivers sun fito kwansu da kwarkwata domin tarbar Atiku Abubakar da tawagara
Source: Twitter

Kamfen: Hotunan ziyarar Atiku jihar Cross Rivers

Filin taro ya cika ya batse da al'umma a jihar Cross Rivers yayin da Atiku Abubakar ya ziyarci jihar domin kamfen
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel