Cikin Hotuna: Osinbajo ya ziyarci iyalan marigayi Manjo Solomon Kabiru Umaru

Cikin Hotuna: Osinbajo ya ziyarci iyalan marigayi Manjo Solomon Kabiru Umaru

Mun samu cewa, a sakamakon kyakkyawa kuma farar aniya ta mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, a safiyar jiya ta Laraba ya gudanar da wani abun son barka cikin garin Abuja da ya cancanci yabo da jinjina.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, yayin ci gaba da shawagin sa na gida-gida, Farfesa Osinbajo ya kai ziyarar bazata gidan Marigayi Manjo Solomon Kabiru Umaru inda ya gana da iyalan sa a yankin Kurudu da ke garin Abuja.

Marigayi Manjo Solomon ya riga mu gidan gaskiya a ranar 17 ga watan Dasumba na shekarar 2014 a fagen fama na yiwa kasar sa hidima yayin yakar ta'addanci a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ga hotunan ziyarar mataimakin shugaban kasa tare da uwargidan Marigayi, Misis Gloria Umaru da kuma 'ya'yayen sa uku; Ruth, Solomon da kuma Sarah.

Osinbajo yayin ziyarar iyalan marigayi Manjo Solomon Kabiru Umaru

Osinbajo yayin ziyarar iyalan marigayi Manjo Solomon Kabiru Umaru
Source: Twitter

Osinbajo tare da Uwargidan marigayi Manjo Solomon da 'ya'yan sa uku

Osinbajo tare da Uwargidan marigayi Manjo Solomon da 'ya'yan sa uku
Source: Twitter

KARANTA KUMA: 2019: Ya kamata yankin Arewa maso Gabas ya samar da shugaban kasa - Dogara

Cikin Hotuna: Osibajo ya ziyarci iyalan marigayi Manjo Solomon Kabiru Umaru

Cikin Hotuna: Osibajo ya ziyarci iyalan marigayi Manjo Solomon Kabiru Umaru
Source: Twitter

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel