Rashin girmama Sultan: Bafarawa ya yiwa Wammako wankin babban bargo

Rashin girmama Sultan: Bafarawa ya yiwa Wammako wankin babban bargo

- Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa ya yi Allah wadai da magajinsa, Sanata Aliyu Wamakko da bisa zarginsa da rashin da'a ga sarkin musulmi Sa'ad Abubakar

- Bafarawa ya ce sarkin musulmin ya gayyacci 'yan takara da jiga-jigan jam'iyyun siyasa zuwa taron zaman lafiya amma 'yan jam'iyyar APC sun ki amsa gayyatar

- Bafarawa ya yi kira da al'ummar jihar Sokoto zu zabi gwamna Tambuwal a karo na biyu domin shine zai kawo cigaba a jihar

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa ya soki magajinsa, Sanata Aliyu Wamakko da dan takarar gwamna na jam'iyyar APC, Ahmed Aliyu Sokoto saboda rashin hallartar taron zaman lafiya da Sultan Muhammad Sa'ad ya kira.

Bafarawa ya yi wannan maganar ne a taron yakin neman zaben Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a garin Wammako.

Rashin girmama Sultan: Bafarawa ya yiwa Wammako wankin babban bargo

Rashin girmama Sultan: Bafarawa ya yiwa Wammako wankin babban bargo
Source: Depositphotos

A cewar tsohon gwamnan, Sarkin musulmin gayyaci dukkan 'yan takara da jiga-jigan jam'iyyun siyasa a jihar ne domin ya basu shawara a kan yadda za su gudanar da kamfe da zabe cikin zaman lafiya amma 'yan jam'iyyar na APC suka ki hallartar taron.

DUBA WANNAN: Jigo a APC ya ce kowa ya zabi abinda ya ke so bayan zaben Buhari

"Na tuna lokacin da Sultan ya kira taron zaman lafiya domin tabbatar da cewa anyi zabi cikin zaman lafiya a jihar nan. Dalilin sa kuwa itace dukkan mu 'yan jiha guda ne kuma ya dace mu tabbatar anyi zabe cikin zaman lafiya.

"Amma abin mamaki shine dan takarar gwamna na jam'iyyar APC ya ki amsa gayyatar wanda hakan ya nuna yana biyaya ga maigidansa Wamakko ne.

Bafarawa ya ce jihar zaman lafiya ta ke bukata ba tashin hankali ba, ya kuma kara da cewa 'komi yana da lokacinsa. Lokaci na ya wuce kuma da Wamakko ya wuce, abinda ya dace shine mu hada kai wuri daya domin gina jihar mu."

Ya tabbatarwa al'ummar garin Wamakko cewa gwamnatin Tambuwal za ta kawo sauki a cikin rayuwansu a dukkan jihar, ya ce zai yiwa al'umma aiki kamar yadda shima ya yi a lokacin da ya ke gwamna.

Tsohon gwamnan ya tabbatarwa matasa cewa gwamnatin Tambuwal za ta mayar da hankali wurin samar musu da ayyukan yi da basu tallafi muddin suka sake zaben sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel