Rigimar duniya: Matashi ya kai karar iyayensa saboda sun haife shi babu izinin sa
Wani matashi mai shekaru 27 da ake kira Raphael Samuel, dan asalin kasar Indiya, ya kai karar iyayensa kotu saboda sun haife shi ba tare da amincewar sa ba.
Raphael ya bayyana cewar yana matukar kaunar iyayen sa amma duk da haka ya gaza fahimtar banbancin da ke tsakanin haihuwar sa da bautar da shi ko yin garkuwa da shi, ya na mai fadin cewar bai ga banbanci tsakanin su ba tun da dukkan su na faruwa ne ba tare da amincewar mutum ba.
Dan asalin birnin Mumbai, Rapahael ya ce rashin adalci ne ga iyaye su haifi mutum don kawai son jin dadin su ko samun farinciki ba tare da yin la’akari da irin wuyar da zai sha a rayuwar duniya ba.
A wata hira da aka yi da shi, Raphael ya ce; “Ina son iyaye na kuma akwai jituwa da shakuwa tsakani na da su, amma sun haife ni ne domin jin dadi da farin cikin su.
“Duk da rayuwata ba a cikin wani kunci ta ke ba, ban ga dalilin da zai sa a haifi mutum don kawai ya zo duniya ya sha wahalar karatu da neman aiki ba, musamman ganin cewar babu amince wa ko yardar sa kafin faruwar hakan.”
DUBA WANNAN: Shigar Atiku Amurka alfarma ce ta wucin gadi - Rahoton Reuters
Matashin na daga cikin matasan kasar Indiya da muryar su ta yi amo wajen yaki da haihuwa. Matasan na kafa hujja da cewar haihuwa na kara yawan matsaloli a rayuwa, musamman ta fuskar albarkatu da duniya ta dogara da su da kuma gurbacewar muhalli.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng