Tinubu ya fara juya mana baya a 2015 bayan mun zauna da shi – Tambuwal

Tinubu ya fara juya mana baya a 2015 bayan mun zauna da shi – Tambuwal

- Aminu Waziri Tambuwal ya bada labarin yadda rikici ya shiga tsakanin su da Bola Tinubu

- Tambuwal yace Tinubu ya saba alkawarin da aka yi da shi a game da zaben Saraki da Dogara

- Gwamnan Sokoton yace Tinubu ya nemi ya kawo su Akume bayan an gama magana da shi

Tinubu ya fara juya mana baya a 2015 bayan mun zauna da shi – Tambuwal
Tambuwal yace sun zauna da Tinubu a gidan sa bayan zaben 2015
Asali: Facebook

Mun ji labari cewa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, yayi bayani game da irin dangantakar sa da babban jigon jam’iyyar APC kuma kusa a tafiyar siyasar kasar Yarbawa watau Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Aminu Waziri Tambuwal yace bayan zaben 2015, shi da gwamnan jihar Zamfara watau Abdulaziz Yari sun yi kokarin zama da Bola Tinubu inda su ka tattauna game da wanda ya dace a nada ya zama shugaban majalisar tarayya.

KU KARANTA: Mataimakin shugaban kasa zai kaddamar da titin dogo daga a Legas

Gwamna Aminu Tambuwal yace a lokacin, sun cin ma matsaya cewa Yakubu Dogara zai zama mataimakin Honarabul Femi Gbajabiamila, wanda jam’iyyar APC a wancan lokaci su ka nunawa goyon baya ya zama Kakakin majalisa.

Aminu Tambuwal yace da kan sa su ka je tare da Abdulaziz Yari su ka samu Bola Tinubu a Legas domin su samu maslaha. Aminu Tambuwal yace sun yi na’am cewa Bukola Saraki zai zama mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Tambuwal yace bayan duk an ci ma wannan yarjejeniya ne kurum sai ya ji labarin cewa Mutanen Bola Tinubu su na neman sabawa wannan tsari da aka yi inda Ahmad Lawan da George Akume su ka fara neman shugabancin majalisar.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ba zai koma kan mulki ba inji ‘Yan Shi’a

Rt. Hon. Aminu Tambuwal yace haka-zalika Tinubu ne ya fara yin watsi da tsarin da aka yi na cewa Femi Gbajabiamila da Yakubu Dogara za su rike majalisa. Gwamnan da yanzu ya koma PDP ya fadawa Jaridar Vanguard wannan.

Tsohon Shugaban Majalisar Tarayyar yace Tinubu ya saba wannan alkawarin da aka yi da shi saboda adawar da ta shiga tsakanin sa da Bukola Saraki. A baya su Saraki ne su ka hana a ba Tinubu kujerar mataimakin shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng