Mataimakin shugaban kasa zai kaddamar da sabuwar hanyar Layin Dogo daga Ogun zuwa Legas

Mataimakin shugaban kasa zai kaddamar da sabuwar hanyar Layin Dogo daga Ogun zuwa Legas

- A gobe Laraba mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo zai bude sabuwar hanyar layin dogo daga jihar Ogun zuwa Legas

- Hukumar kula da harkokin jiragen kasa da layin dogo ta Najeriya, NRC, ta ce Osinbajo zai bude katafaren aikin na layin dogo tun daga birnin Abeokuta kuma ya ratsa ta Ibadan kafin shiga Legas

- Ministan Sufuri ya yabawa ingancin aikin yayin ziyarar gani da ido tare da yabawa bajintar gwamnatin shugaban kasa Buhari kan wannan hobbasa na samar da ci gaba a Najeriya

Mun samu cewa a gobe Laraba da Hausawa ke mata lakabi da Tabawa ranar samu, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo zai kaddamar da wani katafaren aiki na ginin Layin Dogo da aka kammala daga birnin Legas zuwa na Ibadan.

Layin Dogo da Osinbajo zai bude a gobe Laraba

Layin Dogo da Osinbajo zai bude a gobe Laraba
Source: Twitter

Sambaleliyar layin dogo daga birnin Abeokuta zuwa Legas

Sambaleliyar layin dogo daga birnin Abeokuta zuwa Legas
Source: Twitter

Shimfidar layin dogo da za ta ratsa daga birnin Abeokuta da Ibadan zuwa Legas

Shimfidar layin dogo da za ta ratsa daga birnin Abeokuta da Ibadan zuwa Legas
Source: Twitter

Hukumar kula da harkokin jiragen kasa da layin dogo ta Najeriya, Nigerian Railway Corporation, NRC, ita ce ta bayyana hakan a yau Talata cikin wata sanarwa a shafin ta na zauren sada zumunta.

Hukumar NRC ta ce a gobe Laraba Farfesa Osinbajo yayin kaddamar da sabon ginin na layin Dogo zai yi doguwar tafiya daga birnin Abeokuta na jihar Ogun inda zai ratsa ta birnin Ibadan na jihar Oyo kafin ya cimma matsaya a birnin Legas domin tabbatar da ingancin aikin da aka kammala.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Shugaba Buhari yayin rantsar da sabon shugaban hukumar ICPC

Kazalika jaridar Leadership ta ruwaito cewa, Ministan sufuri Rotimi Amaechi, a ranar Litinin din da ta gabata yayin ziyarar gani da ido ya yabawa nagarta gami da ingancin wannan katafaren aiki da gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari ta aiwatar.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnatin shugaba Buhari ta yi kwazo na kammala aikin cikin gaggawa domin rage cunkoso da inganta hanzarin Matafiya yayin sufuri daga jihar Ogun zuwa birnin Legas.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel