Mutuwa ta riski wasu Magoya bayan APC a wajen yakin neman zabe

Mutuwa ta riski wasu Magoya bayan APC a wajen yakin neman zabe

Mun samu labari maras dadi cewa wasu Magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya sun rasu a wani hadarin mota. Wannan mummunan hadari ya auku ne a jiya Ranar Litinin a kan titin jihar Legas.

Manema labarai sun rahoto aukuwar wannan labari mai ban takaici a jiya. Wata mota kirar Jeep samfarin SUV ta kife ne yayin da Direban ta yake dirka gudu. Direban motan yayi kokarin cin ma wasu ‘yan siyasa ne a kan hanya.

Kamar yadda labarin ya zo mana, wannan mota tayi ta kundunbala ne a lokacin da tayi yunkurin riskar tawagar wani Sanatan APC na jihar Legas mai suna Mista Solomon Adeola. Sanata Adeola shi ne ke wakilcin yammacin jihar Legas.

KU KARANTA: PDP ta dage kamfen saboda kisan 'Yar’uwar Sanata a Zamfara

Sanatan na APC ya fitar da jawabi yanzu haka yana mai alhinin wannan mummunan abu da ya auku a hanyar Amuwao zuwa garin Odofin. ‘Dan majalisar ya fitar da jawabi ne ta bakin wani babban Hadimin sa mai suna Cif Kayode Odunaro.

‘Dan majalisar a jawabin da ya fitar, ya nuna jimamin sa na rashin wadannan mutane har 3 da aka yi. Babban Sanatan ya aikawa Iyalin mamatan da ta’aziyyar musamman inda har yayi masu addu’a lokacin da yake yawon kamfe bayan nan.

An dai yi kokari kai mutanen da hadarin da ya auka da su zuwa asibiti, amma ba ayi nasarar ceto rayuwar su ba. Yanzu dai ana daf da gudanar da zaben shugaban kasa ne da ‘yan majalisu a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel