Sai na aske gashi na idan Buhari yayi nasara a zaben 2019 - Bello Muhammad

Sai na aske gashi na idan Buhari yayi nasara a zaben 2019 - Bello Muhammad

Daya daga cikin fitattun jaruman Kannywood, Bello Muhammad Bello da ya fi shahara da inkiyar BMB, ya sha alwashin aiwatar da wani abun ban mamaki yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cimma nasara a babban zaben kasa da zai gudana makonni biyu masu gabatowa.

Fitaccen jarumin wasan kwaikwayo da nishadantar wa na dandalin Kannywood, Bello Muhammad Bello, ya sha alwashin aske sumar sa wato gasun sa na ka muddin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi nasara ta samun tazarcen kujerar sa a babban zabe na bana.

Sai na aske gashi na idan Buhari yayi nasara a zaben 2019 - Bello Muhammad

Sai na aske gashi na idan Buhari yayi nasara a zaben 2019 - Bello Muhammad
Source: Twitter

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, fitaccen jarumin ya zayyana hakan ne cikin wata hira yayin ganawar sa da manema labarai na jaridar Daily Trust dangane da zaben kujerar shugaban kasa da zai gudana a ranar 16 ga watan Fabrairu na shekarar da muke cikin ta a yanzu.

Sakamakon tsagwaran soyayya da ta mamaye ruhin sa da kuma zuciya, ya ce zai aske gasun sa na ka a duk sa'ilin da aka bayar da sanarwar nasarar shugaban kasa Buhari domin jaddada murna da kuma farin ciki.

Jarumi BMB ya ce, akwai sa'ilin da ya hau kujerar naki yayin da wani mai shirin fim ya nemi ya aske sumar sa akan zunzurutun kudi na Naira miliyan daya da rabi domin ya sanya shi cikin wani wasan kwaikwayo.

KARANTA KUMA: Sanatoci da ba za su koma Kujerun su ba a bana

A kalami na sa, "cikin kudira ta wanda ke busa min numfashi na sha alwashin kafa tarihin yashe sumar kai na a duk yayin da sakamakon babban zaben kasa ya ambaci nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari."

Gogaggen jarumi wanda kuma ya kasance mai bayar da umarni a dandalin Kannywood a halin yanzu yana ci gaba da tara gasun sa na ka tsawon shekaru goma da suka gabata ba tare da ko da saisaye ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel