Kamfen din Buhari: Mutane 2 sun suma a jihar Jigawa

Kamfen din Buhari: Mutane 2 sun suma a jihar Jigawa

- A jiya, Asabar, ne shugabannkasa Muhammadu Buhari da tawagar kamfen din jam'iyyar APC su ka ziyarci jihar Jigawa

- Taronkamfen din da aka yi a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, ya samu halartar masoya da magoya bayan shugaba Buhari da jam'iyyar APC

- Majiyar Legit.ng ta tabbatar ma ta da cewar wasu mutane sun suma saboda cikar jama'a a filin da ka gudanar da taron kamfen din

Majiyar Legit.ng ta sanar a ita cewar wasu mutane sun fadi sumammu a wurin taron yakin neman sake zaben shugaba Buhari da aka gudanar jiya, Asabar, a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

A cewar jaridar Daily Trust, an gaggauta fita da wasu mutane da su ka fadi sumammu saboda karancin iskar numfashi da cunkuson jama'a ya haifar a filin taron.

Kazalika rahotanni sun bayyana cewar jami'an tsaro sun gaza shawo kan dandazon jama'ar da su ka halarci taron.

Kamfen din Buhari: Mutane 2 sun suma a jihar Jigawa
Kamfen din Buhari: Mutane 2 sun suma a jihar Jigawa
Asali: Twitter

Jami'an tsaro sun gaggauta bayar da agajin gaggawa ga wani da ya suma ta hanyar kwara ma sa ruwa bayan ya fadi sumamme.

Ma'aikatan lafiya sun gaggauta ficewa da mutum na biyu da ya suma a wurin taron.

DUBA WANNAN: Kamfen: Hudu sun mutu, shida sun samu raunuka a Jigawa

Dubun dubatar masoya da magoya bayan shugaba Buhari da jam'iyyar APC ne su ka halarci taron yakin neman zaben da aka gudanar a Aminu Kano Square da ke garin Dutse, babbab birnin Jigawa.

Shugaba Buhari da tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC sun dira a garin Dutse bayan kammala taron yakin neman zabe a jihar Gombe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel