Shugaban NITDA ya lashe lambar yabo daga Kamfanin Business Day

Shugaban NITDA ya lashe lambar yabo daga Kamfanin Business Day

- A makon jiya ne Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya samu wasu kyaututtuka 2

- Shugaban na Hukumar NITDA ya tashi da kyauta a wajen taron Business Day

- Wani babban Jami’in NITDA ne ya wakilci DG Isa Pantami wajen wani taron

Shugaban NITDA ya lashe lambar yabo daga Kamfanin Business Day

Isa Pantami ne CYBER SECURITY PERSONALITY na shekarar 2019
Source: Twitter

Mun samu labari cewa Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami wanda shi ne shugaban hukumar nan ta NITDA ya samu lashe wasu manyan kyaututtuka a cikin ‘yan kwanakin nan. Ana dai cigaba da yabawa aikin shugaban na NITDA.

A farkon watan nan na Fubrairu ne mu ka ji cewa Dr. Isa Pantami ya lashe kyauta a matsayin shugaban hukumar da ya fi kowa sanin harkar tsaro na yanar gizo. An yabawa kwarewar shugban NITDA din wajen sanin kan aiki.

Kungiyar nan ta The Nollywood Mandate ce ta ba Pantami wannan kyauta inda aka jinjina masa wajen sha’anin shugabanci a gwamnati. Ba dai wannan ba ne karo na farko da Malamin ya samu irin wannan lambar yabo a Najeriya.

KU KARANTA:

Duk a cikin watan nan, mun kuma ji cewa Dr. Isa Ali Pantami ya tashi da kyauta a matsayin babban jami’in gwamnatin da yayi fice a shekarar nan. Wani ma’aikacin hukumar NITDA ne ya karbi wannan kyauta a madadin Isa Pantami.

A kan shirya rana ta musamman wanda ake kira Business Day Excellence, inda a nan ne aka mikawa Ali Pantami lambar girma a cikin sauran Takwarorin sa da ke aikin gwamnati. Hukumar NITDA ta bayyana wannan a makon nan.

Darektan sashen nan na ITIS watau Usman G Abdullahi ne ya wakilici shugaban na NITDA a wajen wannan biki. Isa Pantami wanda malamin addini ne, yana cigaba da nuna bajintar sa a bangaren boko da aikin gwamnati a NITDA.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel