Na cika alkawarin dana dauka a shekarar 2015 – Buhari ga yan Najeriya

Na cika alkawarin dana dauka a shekarar 2015 – Buhari ga yan Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya daki kirji tare da bayyana alfaharin cewa ya cika dukkanin alkawurran daya daukan ma yan Najeriya a lokacin da yake fafutukar neman kuri’unsu yayin yakin neman zaben 2015.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne a ranar Talata, 29 ga watan Janairu yayin da jirgin yakin neman zabensa ya isa jahar Abia da jahar Imo, dukkaninsu jihohi ne dake yankin kudu maso gabas, inda yan kabilar Ibo suka fi yawa.

KU KARANTA: Sallamar Onnoghen: Atiku ya kai korafin Buhari gaban manyan kasashen duniya akan laifuka 5

Filin wasa na kungiyar kwallon kafa ta Enyimba ta yi cikan farin dango a yayin da shugaba Buhari da tawagarsa suka isa garin Aba, babbar cibiyar kasuwanci ta yankin inyamurai gaba daya, duk da umarnin da kungiyar rajin kafa kasar Biyafara, IPOB, ta bayar na cewa kowa ya zauna a gida.

A jawabin daya gabatar a yayin taron, Buhari ya bayyana ma jama’an Ibo cewa idan har suka zabeshi ya samu nasara a zaben 2019, toh zai karkatar da hankalinsa ga samar da manyan ababen more rayuwa, tare da tabbatar da yan Najeriya sun gudanar da kasuwanci cikin sauki.

“A lokacin da muka hau mulki, mun dauki manyan matsaloli guda uku a matsayin abubuwan da muka sanya a gaba, sune tsaro, tattalin arziki da cin hanci da rashawa, mun yi iya bakin kokarinmu daga 2015 zuwayan yanzu wajen cika wannan alkawari.

“Duk da karyewar farashin mai, amma muna gina hanyoyi, muna gina titin jirgin kasa, muna aiki tukuru game da wutar lantarki, wadannan ayyuka ne wanda gwamnatocin da suka gabata basu waiwayesu ba duk da makudan kudaden shigan da suka samu.” Inji shi.

Buhari ya samu rakiyan shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole, tsohon gwamnan jahar Abia, Orji Uzor Kalu, ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu, tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani, tsohon gwamnan Ekiti, Niyi Adebayo, ministan kwadago, Chris Ngige da sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel