2019: Ya zama wajibi Yarbawa su zabi Buhari - Afenifere

2019: Ya zama wajibi Yarbawa su zabi Buhari - Afenifere

Wasu daga cikin mambobin kungiyar Yarbawa ta Afenifere, a yau Talata cikin birnin Ibadan na jihar Oyo, ta wajabtawa dukkanin Yarbawa zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma dukkanin 'yan takara na jam'iyyar APC a yayin babban zabe na bana.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, umarni na wajabcin ya biyo bayan shawarar da wasu jiga-jigan kungiyar suka yanke yayin wata ganawa da suka gudanar a babban dakin taro na kasa-da-kasa da ke jami'ar Ibadan.

Kira na sake zaben Buhari da tabbatar da tazarcen sa ya biyo bayan shawarar Sanata Olabiyi Durojaiye da kuma sauran jagororin kungiyar na jihohi shida da ke yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Buhari yayin yakin neman zaben sa a jihar Imo

Buhari yayin yakin neman zaben sa a jihar Imo
Source: Facebook

Mafi shaharar al'ummar Najeriya da suka halarci taron sun hadar da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, shugaban kungiyar Afenifere na kasa baki daya, Pa Ayo Fasanmi, Sanata Olabiyi Durojaiye da sauran jiga-jigan kungiyar na kasa.

Sauran jiga-jigan Yarbawan sun hadar da tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaji Bola Tinubu, mataimakin gwamnan jihar Oyo, Moses Adeyemo, Yetunde Onanuga ta jihar Oyo, Mista Bisi Egbeyemi da Misis Oluranti Adebule na jihar Legas da sauran su.

Rahotanni sun bayyana cewa, dukkanin masu fada a ji na kabilar Yarbawan sun yi tarayya cikin kira guda na tabbatar da tazarcen shugaban kasa Buhari da kuma Mataimakin sa Osinbajo a yayin babban zaben kasa na watan gobe.

KARANTA KUMA: Tare da duba cancanta, ku zabi 'yan takara daidai da ra'ayin ku - Buhari

Cikin zayyana jawaban sa, Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Buhari ta bai wa yankin Kudu maso Yammacin Najeriya dukkanin hakkin da ya cancanta da a yanzu ya kamata al'ummar yankin su ramawa Kura kyakkyawar aniyar ta.

Mataimakin shugaban kasar ya buga misali dangane da yadda gwamnatin Buhari ta shimfida layin dogo, gine-ginen titi, samar da wutar lantarki da kuma habaka harkokin noma a yankunan Kudu maso Yammacin kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel