Barka: Rahama Sadau ta kammala karatun digiri a wata jami’ar kasar waje (Hotuna)

Barka: Rahama Sadau ta kammala karatun digiri a wata jami’ar kasar waje (Hotuna)

Shahararriyar jarumar wasannin kwaikwayo na harshen Hausa wadanda aka fi saninsu da fina finan Kannywood, Rahama Sadau ta kammala karatun digiri na farko daga jami’ar Eastern Mediterranean dake kasar Cyprus.

Legit.ng ta ruwaito Rahama ce ta bayyana haka a shafinta na kafar sadarwar zamani na Instagram a ranar Talata 29 ga watan Janairu, inda tace ta kammala karatun digiri ne a fannin ilimin tafiyar da ma’aikata.

Barka: Rahama Sadau ta kammala karatun digiri a wata jami’ar kasar waje (Hotuna)

Rahama
Source: UGC

KU KARANTA: Yan bindiga sun yi awon gaba da katuwar mota sukutum, tare da fasinjoji 14 a Najeriya

Daga cikin abubuwan da Rahama ta daura a shafinta na Instagram akwai hotunanta da dama sanye da kayan kammala digiri, inda tace an dauki hotunan ne a yayin da suke gudanar da bikin kammala karatun.

Ita dai Rahama Sadau ta yi fice a fagen taka muhimmiyar rawa a duk matsayin da ta fito a cikin fina finai, walau na fina finan Hausa ko na turanci, wanda hakan yasa likafarta ta cigaba, kuma tauraruwarta ta haskaka.

Barka: Rahama Sadau ta kammala karatun digiri a wata jami’ar kasar waje (Hotuna)

Rahama
Source: Facebook

Daga cikin manyan fina finan da Rahama ta fito akwai wani wanda kamfaninta ta shiryashi, Rariya, haka zalika akwai wani fim na turanci da a yanzu yake tashe a tsakanin masu bibiyan fina finan mai suna ‘Sons of the caliphate’, anan ma Rahama ta taka rawar gani.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel