Gwamnatin jihar Borno za ta tura mafarauta yaki Boko Haram

Gwamnatin jihar Borno za ta tura mafarauta yaki Boko Haram

A yau Litinin ne, Gwamna Kashim Shettima na jihar Borno ya ce gwamnatinsa ta dauki daruruwan mafarauta aiki domin su bayar da gudunmawarsu a yakin da akeyi da 'yan ta'adda a jihar.

Gwamnan ya ce dakarun sojojin Najeriya za su bawa mafarautan horo na gaggawa kafin su fara ayyukan kare iyakar jihar daga harin na 'yan ta'adda.

Mr Shettima ya yi wannan bayanin ne a yayin da ya karbi bakuncin sabon Kwamandan Operation Lafiya Dole, Benson Akinroluyo da ya kai masa ziyarar bangajiya a gidan gwamnati.

Gwamnatin Borno za ta tura mafarauta su yaki Boko Haram
Gwamnatin Borno za ta tura mafarauta su yaki Boko Haram
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Atiku ya lissafa sunayen gurbatattun mutane 30 a cikin gwamnatin Buhari

A cewar Gwamna Shettima, za a girke mahautan a wasu wurare na sirri yayin da gwamnati za ta tabbatar cewar an basu dukkan goyon bayan da kayan aiki da suke bukata.

"A cikin 'yan kwanakin nan, zamu kaddamar da namu rundunar na yaki da 'yan ta'adda wadda ta kunshi 'yan kato da gora da kuma mahauta," inji Shettima.

"Tuni mun basu motocci guda 30 domin tallafawa aikinsu. Kuma zamu mika su ga hannun Hukumar Sojin Najeriya domin taimakawa wurin inganta tsaro da dawo da zaman lafiya a jihar.

"Aikinsu shine inganta tsaro a Maiduguri da kewaye musamman garuruwan da ke kan iyaka.

"Yanzu da zabe ke karatawo, bata gari da yawa za suyi yunkurin kawo tashin hankali domin lalata zaben."

Mr Shettima ya ce hakkin gwamnati ne ta kare rayyuka da dukiyoyin al'umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel