Buhari ya bada umarnin kulle jami’o’I da manyan makarantu 68 na je ka na yi ka

Buhari ya bada umarnin kulle jami’o’I da manyan makarantu 68 na je ka na yi ka

Gwamnatin tarayya ta sanar garkame wasu jami’oi da makarantun gaba da sakandari guda 68 a Najeriya wanda tace an samar dasu ne kawai irin na je ka na yi ka, don haka basa aiki bisa ka’ida, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 27 ga watan Janairu, a yayin da yake ganawa da manema labaru a ofishinsa dake ma’aikatan ilimi a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Samun tagomashi: Jam’iyyu 34 sun yanke hukuncin mara ma Atiku baya a 2019

A jawabinsa, Adamu yace gwamnati ta dauki matakin garkame makarantun ne domin saukaka ma hukumomin kula da makarantu aikinsu tare da kare dalibai daga fadawa hannun mayaudaro masu ha’inci.

Buhari ya bada umarnin kulle jami’o’I da manyan makarantu 68 na je ka na yi ka
Ministan Ilimi Adamu Adamu
Asali: UGC

“Ya dace mu bayyana cewa yayin da wasu daga cikin makarantun ke gudanar da koyo da kayarwa a Najeriya, wasu kuma sun fakewa ne da kasancewa a karkashin wasu makarantun kasashen waje da basu da inganci ko sahhalewar gwamnatin Najeriya.

“Yawaitan ire iren makarantun nan yasa hukumomin dake sa’ido akansu basa iya gudanar da aikinsu yadda ya kamata, bugu da kari yawancin makarantun basa biyan haraji, kuma basa bin dokokin da aka shimfida wajen karantarwa.

“Basa iyakance adadin daliban da suke dauka ko kuma tsarin daukan dalibai, basa neman sahhalewar hukuma kafin su fara karantar da darussa, sa’annan sun yaye baragurbin dalibai, wadanda basu iya samun aiki a ko ina.” Inji shi

Daga karshe Ministan yayi kira ga hukumomin dake sa ido dasu hada kai da hukumomin tsaro wajen tabbatar sun shiga farautan ire iren makarantun nan tare da garkamesu, da kuma gurfanar da mamallakansu gaban kotu.

Hukumomin dake sa ido sun hada da hukumar kula da jami’o’in Najeriya, NUC, hukumar kula da kwalejoji kimiyya da fasaha, NABTEB da kuma hukumar kula da kwalejojin ilimin Najeriya, NCCE.

Wasu daga cikin makarantun daaka kulle sun hada da Jami’ar masana’antu dake Yaba jahar Legas, Jami’ar Blacksmith dake Awka, kwalejin horas da kimiiyar lafiya ta Al-Ameen dake Kaduna, kwalejin horas da kimiyyar lafiya Assam dake Kaduna, kwalejin kimiyya da fasaha ta Bethel dake Benuwe.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng