Gabanin taron yakin neman zabe, Buhari ya gana da Sarakunan gargajiya na jihar Osun

Gabanin taron yakin neman zabe, Buhari ya gana da Sarakunan gargajiya na jihar Osun

- Shugaban kasa Buhari ya shiga zauren majalisa tare da Sarakunan gargajiya na jihar Osun

- Buhari ya yi kira kan hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma

- Shugaban kasar ya jaddada muhimmancin Sarakunan gargajiya wajen ci gaban Najeriya sakamakon kusancin su da al'umma

Gabanin taron yakin neman zaben sa a jiya Asabar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata muhimmiyar ganawa da Sarakunan gargajiya na jihar Osun.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, ganawar tsakanin shugaban kasa Buhari da Sarakunam gargajiya ta gudana ne a babban dakin taro na Banquet dake fadar gwamnatin jihar.

Gabanin taron yakin neman zabe, Buhari ya gana da Sarakunan gargajiya na jihar Osun
Gabanin taron yakin neman zabe, Buhari ya gana da Sarakunan gargajiya na jihar Osun
Asali: Facebook

Shugaban kasa Buhari ya yi kira ga Sarakunan da su daura damarar tallafawa gwamnati a fannin yaki da rashawa da kuma inganta tsaro ta hanyar hada gwiwa da jami'an tsaro musamman na ‘yan sanda sakamakon kusancin su da al'umma.

A kalaman sa, shugaba Buhari yace ganawar sa da Sarakunan gargajiya ta bayu ne wajen neman hadin kan su tare da dukkanin jami'an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma.

KARANTA KUMA: Addini ba zai tasiri ba a zaben gwamnan jihar Kaduna - PDP

Ya kara da cewa, akwai muhimmiyar bukata ta hada karfi da karfe tare da Iyayen kasa wajen tunkarar barazana ta rashin tsaro domin tabbatar da ci gaba da da zai fidda kasar nan zuwa tudun tsira.

Cikin jaddada hadin kansu, Sarakunan sun alwashin jajircewa wajen ci gaba da kwazo da sauke nauyin rawanin su ta hanyar yakar rashawa, jnganta tsaro da kuma tsarkake al'umma daga dukkanin ababen sharri.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel