Mahaifiyar fitaccen dan kwallon kafa na Najeriya, Ahmed Musa, ta riga mu gidan gaskiya
- Sarah Moses, mahaifiyar fitaccen dan kwallon kafa, Ahmed Musa, ta riga mu gidan gaskiya
- Mahaifiyar Ahmed Musa ta riga mu gidan gaskiya bayan ta sha fama da wata 'yar takaitacciyar rashin lafiya
- Ahmed Musa ya ce yau ita ce rana mafi munin bakin ciki a rayuwar sa
A yanzu din nan mun samu rahoton cewa, Sarah Moses, mahaifiyar fittacen dan wasan kwallon kafa na Najeriya, Ahmed Musa, ta riga mu gidan gaskiya a garin Abuja bayan ta sha fama da wata 'yar gajeruwar rashin lafiya.
Ahmed Musa wanda a halin yanzu ya ke taka leda a wata kungiyar kwallon kafa ta kasar Saudiyya, shine ya bayar da sanarwar wannan rahoto na bakin ciki a shafin sa na zauren sada zumunta.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, Marigayi Sarah ta riga mun gidan gaskiya a yau Alhamis 24 ga watan Janairu bayan da sha fama da jinya wani asibiti da ke babban birnin kasar nan na tarayya.
Gabanin cikawar ta, fitaccen ya wallafa wasu sakonni a shafukan sa na zauren sada zumunta, inda ya ke bayyana damuwar sa gami da fatan waraka ga mahaifiyar sa da take fama da rashin lafiya.
KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: An tafka mummunan hatsarin Mota a jihar Legas
Dan wasan ya ce a yau wannan rana ita ce mafi muni a rayuwar sakamakon bakin cikin da ya ke ciki a halin na rashin mahaifiya. Ya ce kewar ta da zai yi ta wuce misali.
Cikin wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, a wannan mako ne fitaccen dan wasan na kungiyar kwallon kafa ta Juventus wato Cristiano Ronaldo, ya amsa laifin sa na zargin kauracewa biyan haraji yayin da ya shura tamola a kasar Spain.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng