Gwamnatin jahar Kaduna ta gina wata katafaren kamfanin sarrafa nono da madara

Gwamnatin jahar Kaduna ta gina wata katafaren kamfanin sarrafa nono da madara

Gwamnatin jahar Kaduna a karkashin jagorancin gwamnan jahar Malam Nasir Ahmad El-Rufai ta kaddamar da wani katafaren kamfanin sarrafa nona da madara a lardin kiwon dabbobi na Ladugga dake cikin karamar hukumar Kachia.

Legit.ng ta ruwaito yar takarar mataimakiyar gwamnan jahar, Dakta Hadiza Balarabe ce ta wakilci El-Rufai a yayin bikin kaddamar da kamfanin daya gudana a ranar Laraba, 23 ga watan Janairu a kauyen Ladugga.

KU KARANTA: Ganduje, Abba da yan takarar gwamna 27 sun shiga yarjejeniyar zaman lafiya a yayin zabe

Gwamnatin jahar Kaduna ta gina wata katafaren kamfanin sarrafa nono da madara
Hajiya Hadiza
Asali: Facebook

Jami’in watsa labaru na ma’aikatar noma da gandun dabbobi, Dahiru Abdullahi ne ya bayyana haka a yayin da yake ganawa da manema labaru, inda yace an samar da kamfanin ne domin inganta kiwon dabbobi da kuma habbaka tattalin arzikin jahar tare da sama ma matasan makiyaya aikin yi.

Gwamnatin jahar Kaduna, tare da hadin gwiwar cibiyar bada tallafi ta kasar Birtaniya, UK-DFID ne suka hada karfi da karfe wajen gina wannan katafaren kamfani da zai iya sarrafa litan nono dari biyar (500Lt) a kowanne rana.

Gwamnatin jahar Kaduna ta gina wata katafaren kamfanin sarrafa nono da madara
Kamfanin
Asali: UGC

A kokarinta na cimma burin samar da kamfanin, tun a shekarar 2015 gwamnatin jahar ta raba ma makiyayan yankin ingantaccen irin ciyawa domin amfanin dabbobinsu, mai suna ‘Napier’, wanda ya kara adadin nonon da suke samu daga dabbobinsu da kashi 100.

Manufar wannan kamfani shine nuna ma makiyaya amfanin kiwon dabbobinsu a waje daya ba tare da sun yi ta fita yawon kiwo wanda a dalilin haka suna shiga gonakan manoma ana samun hatsaniya ba.

Gwamnatin ta saya ma kamfanin babura da tukunyar amsan nono, da kuma kekuna na tallar madarar yayin da aka kammala sarrafata. Daga karshe gwamnati a fata yan kasuwa da masu hannun zuba jari su zuba jari a harkar sarrafa nona ta yadda za’a inganta kiwo tare da habbaka tattalin arzikin jahar baki daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng