Birnin Kebbi: Jama'a sun cika da murna, farincikin zuwan Buhari
Dubban jama'a da su ka hada da manya, kanana, da matasa sun cika da murna da farinciki bayan tawagar yakin neman zaben shugaba Buhari ta isa Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi.
Dumbin masoya da magoya baya ne su ka tarbi shugaba Buhari tun daga filin jirgin sama bayan saukar sa, su ka kuma raka shi har cikin gari.
Taron jama'ar, sun mamaye tituna tare da rera wakar "sai Baba".
Tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC da dan takarar ta na shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta bar garin Sokoto zuwa Birnin Kebbi, bababn birnin jihar Kebbi, domin kaddamar da yakin neman zabe.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar shugaba Buhari da tawaga sa sun fara ziyartar fadar mai alfarma sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III, kafin su karasa zuwa filin wasan da aka yi taron kamfen din APC a jihar Sokoto.
Da yake magana cikin yaren Hausa ga dubban jama'ar da su ka halarci wurin kamfen din, shugaban Buhari ya bukaci masoya da magoya bayan APC su kada kuri'un su ga dukkan 'yan takarar jam'iyyar a zabe mai zuwa.
Buhari ya ce gwamnatin APC ta yi rawar gani a bangarorin yaki da cin hanci, inganta tsaro, da bunkasa tattalin arziki.
Da ya ke kara jaddada niyyar sa ta ganin an gurfanar duk wadanda ake zargi da almundahana da dukiyar jama'a, Buhari ya shaida wa jama'a cewar ba zai taba cin amanar yarda da shi da 'yan Najeriya su ka yi ba.
DUBA AWANNAN: Kamfen din APC: Hudu sun mutu, shida sun samu raunuka a Jigawa
Kazalika, ya nuna jin dadinsa bisa yadda aka samu kyawun amfanin gona da yadda manoma su ka samu riba a cikin shekaru biyu da su ka wuce, tare da yin kira ga jama'a da su rungumi harkokin noma.
"Muna godiya ga Allah bisa samun wadataccen ruwan damina da ya saka amfanin gona yin kyau a shekarar 2017 da 2018," a kalaman Buhari.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng