Babu wanda ya isa ya sa ayi murdiya a zaben bana inji Shugaban INEC Yakubu

Babu wanda ya isa ya sa ayi murdiya a zaben bana inji Shugaban INEC Yakubu

Dazu ne mu ka ji labari cewa hukumar zabe na kasa watau INEC ta maida martani a kan kalaman tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo wanda yace da wuya hukumar ta iya shirya zaben kwarai a bana.

Babu wanda ya isa ya sa ayi murdiya a zaben bana inji Shugaban INEC Yakubu
Hukumar INEC tace za ta gudanar da zabe na kwarai a bana
Asali: Facebook

Shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Mahmoud Yakubu, da kan sa ne ya karyata Cif Olusegun Obasanjo inda yace babu wani matsin lamba da ke kan hukuma ta INEC na shirya abin da ba daidai ba a zaben da ke karatowa a kasar.

Shugaban na INEC yayi wannan jawabi ne lokacin da ya gana da sabon sufeta janar na ‘yan sandan Najeriya domin ganin yadda za a shawo kan zaben kasar. Yakubu yake surutun da ake yi na shirin murde zabe, sam ba gaskiya bane.

KU KARANTA: An yi wa Buhari alkawarin kuri’a masu tsoka a Jihar Nasarawa

Ana tunani dai Farfesa M. Yakubu yana maida martani ne ga Olusegun Obasanjo inda yake cewa babu abin da zai sa hukumar zabe ta zubar da kimar ta mutuncin ta a zaben na 2019 ta hanyar yin abin da bai dace ba saboda son rai.

Mahmood Yakubu wanda ke shugabantar INEC din yace za su yi aiki da jami’an tsaro da kuma ‘yan jarida wajen ganin an yi keke-da-keke a zaben da yake gabatowa. Yakubu yace babu wanda ya isa ya matsawa INEC tayi murdiya.

Shugaban hukumar na INEC ya kara tabbatarwa Duniya cewa za ayi zaben gaskiya a Najeriya inda kuri’ar kowa za tayi tasiri a Najeriya. A baya dai dai INEC din ta bada irin wannan tabbaci game da zaben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel