Jama’an jahar Yobe sun yi fitar farin dango wajen tarbar Buhari yayin da ya shiga Damaturu

Jama’an jahar Yobe sun yi fitar farin dango wajen tarbar Buhari yayin da ya shiga Damaturu

Da tsakar ranar Litinin, 21 ga watan Janairu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa garin Damaturu, babban birnin jahar Yobe, don cigaba da ganawa da masoya da magoya bayan jam’iyyar APC a yakin neman sake zabensa da yake yi.

Buhari ya isa garin Damaturu ne da misalin karfe 2:15 na rana, jim kadan bayan ya fito daga garin Maiduguri na jahar Borno, inda a can ma yayi gaba da gaba da dimbin masoyansa da suka yi fitar farin dango wajen tarbarsa.

KU KARANTA: Ta fallasa: Yadda na kai ma Fayose $5,000,000 daga cikin kudin makamai – Tsohon Minista

Jama’an jahar Yobe sun yi fitar farin dango wajen tarbar Buhari yayin da ya shiga Damaturu
Buhari
Asali: UGC

Kai tsaye jirgin Buhari ya sauka a cikin fadar gwamnatin jahar Yobe dake garin Damaturu, tare da shugaban jam’iyyar APC, Aliyu Adams Oshiomole, jagoran APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, daraktan yakin neman zabensa, Rotimi Amaechi da sakatariyarsa Hadiza Bala Usman.

Tawagar shugaba Buhari ta samu kyakkyawar tarba daga gwamnan jahar Yobe, Ibrahim Gaidam, sakataren APC kuma dan takarar gwamnan jahar a inuwar jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, karamar ministar harkokin kasashen waje, Khadija Bukar Abba, shugaban NEMA, Mustapha Maihaja.

Sauran sun hada da kafatanin yan majalisun dattawa, wakilai da na dokokin jahar yan jam’iyyar APC, kwamishinoni, mashawartan gwamna da sauran masu rike da mukaman siyasa, kamar yadda Legitng ta ruwaito.

Da misalin karfe 3:30 Buhari ya isa filin wasa na garin Damuturu, inda ya gabatar da jawabi ga zunzurutun jama’an da suka kwashe sa’o’I da dama a cikin rana dan yin ido hudu da shi, majiyarmu ta ruwaito an rufe kasuwanni, makarantu da ma’aikatu domin ziyarar ta Buhari.

Shima da yake nasa jawabin, shugaban hukumar bada agajin gaggawa, Mustapha Maihaja ya bayyana cewa zaman lafiyan da aka samu a jahar Yobe tasa Buhari ya samu karbuwa dari bisa dari a jahar, don haka yana sa ran Buhari zai cinye jahar gaba daya.

Daga cikin mawakan da suka nishadantar da dandazon jama’an da suka fito wajen ganganin sun hada da Fati Nijar, Dauda Kahutu Rarara, da kuma Kamilu, kuma daga ganin yadda jama’a ke bin wakokin ya nuna sun nishadantu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel