Da duminsa: Buhari ya cire sakataren TETfund, Baffa Bichi

Da duminsa: Buhari ya cire sakataren TETfund, Baffa Bichi

Shugaba Muhammadu Buhari ya cire babban sakataren Asusun tallafawa manyan makarantu (TETFund), Dr. Abdullahi Baffa Bichi.

The Sun ta ruwaito cewa an maye gurbinsa ne da tsohon sakataren hukumar, Farfesaa Elias Suleiman Bogoro.

Kafin nadinsa a matsayin sakateren hukumar tare da wasu shugabanin hukumomi 14 a ma'aikatar ilimi a ranar 2 ga Augustan 2016, Baffa ya kasance hadimi ne ga Ministan Ilimi na kasa, Adamu Adamu.

Da duminsa: Buhari ya cire sakataren TETfund, Baffa Bichi
Da duminsa: Buhari ya cire sakataren TETfund, Baffa Bichi
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Zabe: Dalilin da yasa Amurka ke goyon baya na - Atiku

Wata kwakwarar majiya ta tabbatar da cewa cikin 'yan kwanakin nan, ana samun rashin jituwa tsakanin Baffa da ministan Ilimi, Adamu Adamu musamman dangane da kudaden tallafi na 2019.

An ce ba su jituwa da ministan a kan batutuwa da yawa da ake gudanarwa a karkashin TETFund musamman batun kudaden tallafin jami'o'i.

Bugu da kari, Baffa ya kasance yana shiga cikin harkokin siyasar jihar Kano dumu-dumu gabanin babban zaben da ke tafe a watan Fabrairu.

Ku cigaba da biyo mu domin samun karin bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel