Minista yayi wa Tsohon Sanatan Kaduna raddi bayan ya soki Gwamnatin Buhari

Minista yayi wa Tsohon Sanatan Kaduna raddi bayan ya soki Gwamnatin Buhari

Mun ji labari cewa Ministan harkokin matasa da kuma wasanni na Najeriya watau Solomon Dalung sun kara da wani wanda ya taba neman shugaban kasa a jam’iyyar PDP watau Dr Yusuf Datti Baba-Ahmed.

Minista yayi wa Tsohon Sanatan Kaduna raddi bayan ya soki Gwamnatin Buhari
Tsohon Sanatan yankin Kaduna ya soki Gwamnatin Buhari
Asali: Facebook

A jiya ne jaridar Daily Trust ta shirya wani gagarumin muhawara a garin Abuja inda Dr. Baba-Ahmed ya zargi gwamnatin Buhari da yaudarar jama’a. Sai dai wannan kalamai ba su yi Ministan kasar Solomon Dalung dadi ba.

Dalung yayi tir da yadda tsohon ‘dan takarar na PDP yayi wa gwamnatin APC wannan mummunan zato inda yace Dr. Baba-Ahmed bai yi wa yunkurin da wannan gwamnati ta ke yi na maganin barayi a fadin Najeriya adalci ba.

Baba-Ahmed yake cewa wata jam’iyya da ke yaki da cin hanci ta ware kudi har Naira Biliyan 30 domin a murde zaben 2019. B.Ahmed yace jam’iyyar za ta saki kusan N250, 000 a kowane tashar zabe fiye da 120, 000 da ake da su.

KU KARANTA: Bayan dogon ce-ce-ku-ce, Atiku ya taka kasa a cikin Amurka

Yusuf Baba-Ahmed ya soki yadda shugaban kasa Buhari ya ki amincewa da sabon kudirin zaben kasar. Tsohon ‘dan majalisar ya kuma koka da yadda aka jefa matasa cikin hali na ban tausayi ta hanyar hana su ilmi da yaudarar su.

Solomon Dalung ya maidawa shugaban makarantar nan ta Baze da ke Abuja martani a kan sukar gwamnatin Buhari da yayi. Ministan yace Baba Ahmed yana jin haushi ne kurum domin Atiku ya tika shi da kasa wajen takarar PDP.

Farfesa Jibrin Ibrahim na cibiyar CDD ne ya jagoranci zaman da aka yi inda mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III ya zama babban bako. Maryam Uwaisu tana cikin wadanda suka yi jawabi a wajen taron.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng