Shugaba Buhari yayi magana a kan zaben 2019, zargin Ganduje da Gwamnatin PDP a wajen muhawarar #TheCandidates
A jiya ne Muhammadu Buhari da kuma mataimakin sa Yemi Osinbajo su kayi wa Duniya jawabi game da kamun ludayin gwamnatin APC da su ke jagoranta. Wata gidauniya ce dai ta tsara wannan shiri da aka yi a idon kowa a Abuja.

Asali: Facebook
Sahara Reporters ta tsakuro wasu kadan daga cikin abin da aka fahimta game da sha’anin gwamnatin Buhari:
1. Osinbajo ne bakin Gwamnatin Buhari
A wajen wannan muhawara, an ga yadda Yemi Osinbajo yake ta bada amsoshi yana dogoyen jawabai game da gwamnatin Buhari. Kusan sai daga karshen tattaunawar ne shugaba Buhari ya rika magana sosai.
2. Osinbajo ya kama hanyar Shugaba Buhari
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya bi layin shugaba Buhari na gujewa nauyin tabarbarewar abubuwa ta hanyar daura laifin a kan gwamnatocin baya da jam’iyyar APC ta kifar a 2015.
KU KARANTA: Da kamar wuya a ce zan sha kashi a zaben 2019 – Shugaba Buhari
3. Buhari ya kware a wajen shatale-tale
Shugaban kasa Buhari ya iya kaucewa tambayar da ba ya son amsawa kamar yadda aka rika gani jiya inda ya rika yin hagu yayin da ake yin dama a kan batutuwan da su ka shafi cin hanci da sauran su.
4. Tsohon SGF yana cigaba da cin karen sa babu babbaka
A jiya ne aka tabbarar da cewa duk da shugaba Buhari ya tsige Babachir Lawal daga mukamin Sakataren gwamnatin sa, har yanzu babu niyyar damke sa domin a hukunta, duk da cewa an same sa da laifi dumu-dumu.
5. Kunnen Shugaba Buhari ba ya aiki da kyau?
Sau da-dama an ga alamun cewa akwai matsala a kunnen shugaba Buhari domin kuwa a wasu lokutan sai dai Mataimakin sa ya rika fada masa abin da ake cewa. A baya shugaban kasar ya koka da lalurar jin sa.
6. Akwai Gwamnoni marasa gaskiya a gwamnatin APC
Shugaban kasar ya koka da cewa wasu Gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi su na daga cikin matsalolin kasar nan duba da yadda harkar ilmi ya tabarbare a matakin Firamare
7. Gum game da barnar wasu Makiyaya a kasar
Shugaba Buhari bai yi tir da ta’adin da wasu Makiyaya ke yi a kasar ba, sai dai ya koka da yadda jama’a su ka karbe wuraren kiwon Makiyayan da ke kasar musamman a Kudancin Najeriya.
KU KARANTA: Hankali kwance shugaba Buhari zai yi nasara a zaben 2019
8. Gwamnati na ci da yara fiye da miliyan 10 kullum
Matimakin shugaban kasa Osinbajo ya bayyanawa jama’a yadda su ke taimakawa ‘Yan makaranta da abinci. Osinbajo yace Gwamnatin APC ta na ciyar da Yara fiye da miliyan 10 duk ranar Duniya.
9. Gwamnatin Jonathan tayi tabargaza
Shugaba Buhari da mataimakin sa sun zargi PDP da sace dukiyar Gwamnati a lokacin zave. Osinbajo ya kuma yi kaca-kaca da tsarin SURE-P wanda a cewar sa bai yi wani tasiri na rage talauci a kasar ba.
10. Kudin da aka narka a tsarin Trader Moni
Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bayyana cewa sun bada bashin N10, 000 ga ‘yan kasuwa har 20, 000 ta tsarin nan na Trader Moni. Yanzu haka ana cigaba da ganin amfanin wannan tsari da zai ci Biliyan 20 saboda tausayin talakawa na Gwamnatin APC.
KU KARANTA: Matar Bukola Saraki tayi Allah-wadai da duk 'yan siyasar Najeriya
11. Zargin da ke kan wuyan Ganduje na APC
Buhari yayi magana a kan bidiyon da aka ga gwamna Abdullahi Ganduje yana karbar rashawa inda ya nuna shakkun cewa watakila an yi amfani da siddabarun fasaha na zamani wajen yi wa gwamnan sharri.
12. Buhari ya samu lafiya zam-zam yanzu
Shugaba Buhari ya bayyana cewa ya samu koshin lafiya a halin yanzu inda yayi kira ga jama’a su duba yadda yake yawo a ko ina. Sai dai a jiya ne shugaban kasar ya nemi ya zame a wajen wani taro.
Shugaban kasar yayi magana game da sha’anin Boko Haram da kuma yadda ya fadi zaben 2003, 2007 har da ma 2011 inda yayi ta fama da shari’a a kotun koli kafin yayi nasara a karshe a zaben 2015.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng