Magajin Sarkin Ningi ya riga mu gidan gaskiya

Magajin Sarkin Ningi ya riga mu gidan gaskiya

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, a yau Laraba 16 Janairu, 2019, ajali ya katse hanzarin Muhammad Yunusa Muhammad, babban da ga Sarkin Ningi na masautar jihar Bauchi, Alhaji Yunusa Muhammadu Danyaya.

Alhaji Muhammad Yunusa Muhammad, mai sarautar gargajiya ta Yariman Ningi, ya riga mu gidan gaskiya a safiyar yau ta Laraba cikin garin Bauchin Yakubu.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, an gudanar da jana'izar Marigayi Muhammadu a fadar mahaifin sa da ke garin Ningi a bisa tsari da kuma tafarki irin na addinin Islama.

Magajin Sarkin Ningi ya riga mu gidan gaskiya
Magajin Sarkin Ningi ya riga mu gidan gaskiya
Source: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa, kusoshin gwamnati da dama na jihar Bauchi da suka hadar da shugaban jam'iyyar APC reshen jihar, Alhaji Uba Nana sun halarci jana'izar tare da jajantawa Sarki Danyaya.

Gwamnan jihar Muhammad Abdullahi Abubakar, yayin mika sakon sa na ta'aziya da jajantawa, ya bayyana rasuwar Yariman Ninga a matsayin babban rashi ga masarautar da kuma jihar Bauchi baki daya.

Marigayi Muhammadu gabanin rasuwar sa ya kasance tsohon sakataren gwamnatin jihar Bauchi na dindindin.

KARANTA KUMA: Saduwa da iyali a kan kari yana kara kaifin kwakwalwa - Masana

Yayin ganawar sa da manema labarai, Danburam Ningi, Alhaji Yusuf Yunusa Danyaya, ya ce cutar Asma ce ta yi sanadiyar ajalin dan uwan sa.

A makon da ya gabata, jaridar Legit.ng ta kawo muku rahoton rasuwar sarkin garin Lafiya na jihar Nasarawa, Alhaji Isa Mustapha Agwai I, da ya riga mu gidan gaskiya bayan ya shafe tsawon shekaru 43 a bisa kujerar mulki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng