Zan canja gwamnan babban bankin kasa idan na ci zabe - Atiku

Zan canja gwamnan babban bankin kasa idan na ci zabe - Atiku

- Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, ya ce zai canja babban gwamnan CBN, Godwin Emefiele, idan ya zama shugaban kasa

- Dan takarar ya ce Emefiele ba ya yin abinda ya dace a matsayinsa na gwamnan babban bankin kasa (CBN)

- Kazalika, ya ce zai fito da kudi domin bunkasa kasuwanci da bangaren masana'antu da saka hannun jari

Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce zai canja gwamnan babban bankin kasa (CBN), Gowin Emefiele, sannan ya fito da kudi domin bunkasa kasuwaci idan ya ci zaben da za a yi a wata mai zuwa.

"Godwin Emefiele ba ya yin aikinsa da kyau," a cewar Atiku, sannan ya kara da cewa zai canja gwamnan babban bankin da zarar wa'adinsa ya kare a watan Yuni na shekarar nan.

Atiku na wadannan kalamai ne yau, Laraba, a jihar Legas yayin wata hira da jaridar Bloomberg.

Zan canja gwamnan babban bankin kasa idan na ci zabe - Atiku
Gwamnan babban bankin kasa; Godwin Emefiele
Asali: Twitter

"Ban yarda yana afani da tsarin da zai kawo gyara a tattalin arzikin kasa ba. Dole mu kawo mutane da suka san aiki fiye da shi," a cewar Atiku

DUBA WANNAN: Karin albashi: Gwamnatin tarayya ta amince da biyan N30,000

A bisa shawarar Emefiele ne gwamnatin tarayya ta tsuke bakin aljihunta tare da mayar da hankali wajen bunkasa masana'antun cikin gida.

Gwamnan babban bankin ya sha bayyana cewar ta wannan hanyar ne kadai za a yi maganin matsalar harhawar farashin kayayyaki.

Sai dai masana tattalin arziki da masu saka hannun jari daga kasashen ketare na yawan sukar CBN a kan matsalar rashin tasayar da farashi kudin kasashen waje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng