Ana dara ga dare yayi: Ma’aikata sun fara yajin aiki a wannan jahar kwanaki 30 kafin zabe

Ana dara ga dare yayi: Ma’aikata sun fara yajin aiki a wannan jahar kwanaki 30 kafin zabe

Kafatanin ma’aikatan gwamnatin dake jahar Oyo sun ki fita a aiki a ranar Karaba 16 ga watan Janairu biyo bayan wani yajin aiki da suka kaddamar na tsawon kwanaki uku ba tare da yankewa ba, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ma’aikatan sun shiga yajin aikin ne sakamakon rashin biyansu alawus na karin girma da aka yi musu tun da dadewa, da kuma wasu hakkoki da suka ce suna bin gwamnatin jahar bashi.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Shugaba Buhari ya shilla garin Lokojan jahar Kogi

A zagayen da majiyarmu tayi ta lura cewa duk wasu ofisoshin ma’aikatan gwamnati a garkame suke, haka zalika babbar sakatariyar ma’aikatan jahar ma a kulle take babu wani dake tafiya a cikinsu.

Haka zalika an hangi daruruwan daliban makarantun gwamnati suna komawa gida yayin da malamansu suka fada musu babu makaranta daga yau har zuwa Juma’a, su koma gida, kamar yadda wani dalibi ya tabbatar.

A zantawar da aka yi da wasu ma’aikatan jahar, sun bayyana cewa wajibi su gudanar da wannan yajin aikin domin nuna bacin ransu da yadda gwamnan ke sakwa sakwa da hakkokin ma’aikata.

“Gwamna na wasa da hankulanmu, a baya yayi alkawarin biyanmu hakkokinmu a watan Satumbar data gabata, amma a lokacin da muka tunkareshi da maganar, sai yace mu yi hakuri sai a watan Janairu, muka kara tuna masa, sai ya dinga bamu wasu uzururruka marasa kan gado, Don haka ba zamu sake lamunta ba.” Inji ma’aikacin.

Sai dai duk kokarin da majiyarmu tayi na jin ta bakin shugaban kungiyar kwadago na jahar Oyo yaci tura, sakamakon baya daukan duk kiraye kirayen da aka yi masa ta lambar wayarsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel