Da dumi dumi: Shugaba Buhari ya shilla garin Lokojan jahar Kogi

Da dumi dumi: Shugaba Buhari ya shilla garin Lokojan jahar Kogi

A yanzu haka shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa garin Lokoja na jahar Kogi inda zai gana da yan jam’iyyar APC da magoya bayansa a yayin da zai kaddamar yakin neman zabensa a jahar.

Legit.ng ta ruwaito da misalin karfe sha biyu da yan mintoci jirgin Buhari ya tashi daga fadar shugaban kasa, sai dai irin jirgin nan ne da ake kira da suna ‘Mai saukan Angulu’, a cikinsa ne Buhari nufi garin Lokoja.

KU KARANTA: Rundunar Yansandan Najeriya ta kama wani mutum da laifin kokarin kashe kansa

Da dumi dumi: Shugaba Buhari ya shilla garin Lokojan jahar Kogi
Yayin da jirgin Buhari ya tashi
Asali: Facebook

Haka zalika Buhari ya soke zuwa garin Ilorin na jahar Kwara sakamakon fasa gudanar da yakin neman zaben nasa a yau da jam’iyyar APC ta yi, APC ta fasa gudanar da yakin neman zaben ne biyo bayan rikicin daya barke yayin da wasu yan jagaliya suka afka ma gidan Sanata Bukola Saraki.

An yi asarar rayuka da dukiyoyi a yayin wannan rikici daya barke tsakanin magoya bayan Saraki da abokan hamayyarsa, wannan takaddama yasa gwamnatin jahar ta saka dokar ta baci akan duk wani gangamin siyasa a fadin jahar.

Jadawalin yakin neman zaben shugaba Buhari ya nuna dan takarar na shugaban kasa a jam’iyyar APC zai isa jihohin Edo da Delta a ranar Alhamis 17 ga watan Janairu, inda anan ma zai gana da masoya da kuma yayan jam’iyyar tare da bayyana musu ayyukan alherin daya shimfida musu da kuma sabbin alkawurra.

Sai kuma a ranar Juma’a 18 ga watan Janairu shugaba Buhari zai yi ma jahar Kaduna dirar mikiya, jahar daya samu sama da kuri’u miliyan daya a zaben shekarar 2015, kuma ko a ranar Talata sai da gwamnan jahar Nasir El-Rufai ya tabbatar masa da cewa gaba daya kuri’un jahar Kaduna tashi ce.

A wani labarin kuma, shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo zasu halarci wani taro da zai gudana a babban birnin tarayya Abuja, inda zasu tattauna da yan Najeriya.

Za’a gudanar da wannan taro ne da misalin karfe 8 na daren Laraba 16 ga watan Janairu a dakin taro na Ladi Kwali dake otal din Sheraton, inda Buhari da Osinbajo zasu gana da yan Najeriya tare da sauraron ra’ayinsu na tsawon awanni biyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel