Dandanlin Kannywood: Ina nan da raina, ban mutu ba – Inji Sani Garba SK

Dandanlin Kannywood: Ina nan da raina, ban mutu ba – Inji Sani Garba SK

Shahararren jarumin fina finan Hausa da tauraruwarsa ta haskaka, Sani Garba SK ya musanta rahotanni da ake watsawa a kafafen sadarwar zamani ta Facebook dake cewa wai ya mutu, ya rigamu gidan gaskiya a daren Litinin, 14 ga watan Janairu.

Idan za’a tuna Legit.ng ta buga a shafinta na Facebook cewa ta samu rahoton mutuwar jarumin, sai dai cikin wata hira da gidan rediyon BBC Hausa ta yi da SK a ranar Talata 15 ga watan Janairu, ya musanta wannan labari.

KU KARANTA: Gobara ta tafka ma dalibai mummunar barna a wata babbar makaranta dake Kaduna

Dandanlin Kannywood: Ina nan da raina, ban mutu ba – Inji Sani Garba SK
Sani Garba SK
Asali: UGC

Cikin wannan hira, SK yace yana nan da ransa, kuma yana samun saukin rashin lafiyar da yake fama da ita, ya kara da cewa jama’a da dama sun kirashi a waya don tabbatar da labarin mutuwar, kuma ya shaida musu ba gaskiya bane.

Sai dai jarumin ya tabbatar da cewa yana fama da cutar ciwon siga, kuma likitoci a asibiti ne suka tabbatar masa da wannan lalura da yake fama da ita, don haka mu anan muna yi masa fatan alheri, kuma Allah Ya bashi lafiya.

Ko a kwanakin baya an samu kwatankwacin irin wannan labari, inda aka yayata batun mutuwar shima wani shahararren jarumin Kannywood, Sani Moda, wanda daga bisani ya karyata labarin, sai dai shima yayi fama da rashin lafiya a baya.

A wani labarin kuma, a wannan watan Janairu ne marigayi Ahmad S Nuhu ya cika goma sha biyu da rasuwa bayan rasuwarsa a ranar 5 ga watan Janairu na shekarar 2007 yayin da motarsu ta gamu da hatsari akan hanyarsa ta zuwa garin Azare don gabatar da wasan Sallah.

Ahmad na daga cikin fitattun yan wasan Hausa guda shida da har bayan mutuwarsu tauraruwarsu bata daina haskakawa ba, sauran sun hada da Rabilu Musa Ibro, Aisha Dan Kano, Amina Garba Dumba, Hauwa Maina da Balaraba Muhammad.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel