PDP sun dauko hayar tsohon Shugaban INEC domin murde zabe – APC

PDP sun dauko hayar tsohon Shugaban INEC domin murde zabe – APC

Wani babban jami’in jam’iyyar APC mai mulki ya bayyana cewa jam’iyyar hamayya ta PDP ta na da shirin murde zaben da za ayi. Jami’in na APC ya bayyana wannan ne jiya a cikin Garin Abuja.

PDP sun dauko hayar tsohon Shugaban INEC domin murde zabe – APC

Yekini Nabena yace Atiku ya sayi wani tsohon jami’in INEC
Source: Twitter

Mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa watau Mista Yekini Nabena yana zargin PDP da cewa ta dauko hayar wani tsohon shugaban hukumar zabe na kasa watau INEC domin yayi mata aiki a zaben da za ayi.

Yakini Nabena yayi wannan jawabi ne lokacin da ya zanta da wasu manema labarai a babban birnin tarayya Abuja a Ranar Lahadi inda ya kalubalanci ‘dan takaran PDP, Atiku Abubakar ya karyata wannan zargi da ya rataya masa.

Nabena yana ikirarin cewa kafin nan, PDP tayi kokarin yin aiki da wasu mutanen Kasar waje domin ganin an yi wa shafin yanar gizo na hukumar zabe na kasa watau INEC kutse domin a samu hanyar murde sakamakon zabe.

KU KARANTA: An fara bankado shirin da ‘yan siyasa ke yi wajen murde zaben Najeriya

Jami’in na APC ya ki bayyana sunan wannan tsohon ma’aikacin INEC da zai yi wa jam’iyyar PDP aiki. Sai dai ya nuna cewa yana cikin wadanda su ka rika taimakawa PDP wajen murde zabukan da aka yi a shekarun baya a Najeriya.

Babban Sakataren na APC yace shirin PDP shi ne wannan tsohon Jami’i na INEC yayi amfani da sanayyar sa mutanen sa wajen ganin tsofaffin yaran sa da ke hukumar sun murdewa APC kuri’iun da za ta samu a zaben da za ayi.

Mista Yekini Nabena ya kuma yi watsi da surutan da ake yi game da mukamin da aka ba Amina Zakari, wanda a cewar sa wata dabara ce ta PDP kurum wajen kauda hankalin jama’a daga abin da ya dace a maida hankali a kan sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel