Cigaba: Matashi ya kirkiri bokitin dafa ruwa mai amfani da wutar lantarki a Kaduna, hotuna

Cigaba: Matashi ya kirkiri bokitin dafa ruwa mai amfani da wutar lantarki a Kaduna, hotuna

A yayin da jama'a da dama ke amfani da bokitin fenti domin ajiyar ruwa, wasu matasa a kasuwar Panteka dake jihar Kaduna sun yi amfani da kwakwalwar su wajen mayar da bokitin na dafa ruwa.

Wani dan Najeriya, Mista Jude Ehiabhi, ne ya fara kirkirar bokitin da ya samu karbuwa a kasuwar bajakolin kasa da kasa ta jihar Legas, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.

Wakilin NAN da ya ziyarci kasuwar bajakolin ya ce fasahar matashin ta matukar burge jama'a, kuma jama'a sun sayi bokitin domin amfani da shi a gidajensu.

Cigaba: Matashi ya kirkiri bokitin dafa ruwa mai amfani da wutar lantarki a Kaduna, hotuna
Bokitin dafa ruwa mai amfani da wutar lantarki
Asali: Facebook

Cigaba: Matashi ya kirkiri bokitin dafa ruwa mai amfani da wutar lantarki a Kaduna, hotuna
Bokitin dafa ruwa masu amfani da wutar lantarki
Asali: Facebook

Mista Ehiabhi, mai shekaru 37, ya ce ya faru samun tunanin kirkirar bokitin ne shekaru 7 da suka wuce bayan ya kasa samun sukunin cigaba da karatun jami'a.

"Ina gyaran buta da kofin dafa ruwa a gida, sai nayi nazarin yadda ake jona karfen dake amfani sauka zafi har ruwa ya yi zafi. Watarana kawai sai nayi tunanin saka karfen na like shi a jikin bokiti.

"Da farko ban yi tunanin fasahar zata burge jama'a ba, amma da na fara sayarwa da daidaikun jama'a sai na fahimci abun ya kayatar da su.

"Da ina da hali, da na cigaba da karatu domin samun isashshen ilimin da zan inganta fasahar da nake da ita," a cewar Mista Ehiabhi.

DUBA WANNAN: Fasaha: An fara koyawa matasa a arewa gini da roba

Thomas Ola, wani dan kasuwa da wakilin NAN ya tattauna da shi a wurin sayen bokitin, ya ce fasahar ta matukar burge shi.

"Fasahar ta matukar kayatar da ni, saboda bokitin ko dison ruwa baya fita daga kofar da aka manne karfen dake jiki. Gaskiya akwai mutane masu basira a Najeriya," a cewar Ola.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel