2019: Ku zabi Buhari, kungiyar Izala ta umurci 'ya'yanta

2019: Ku zabi Buhari, kungiyar Izala ta umurci 'ya'yanta

- Kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a Waikamatus Sunnah, JIBWIS ta yi kira ga mambobinta su zabi shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019

- Kungiyar ta ce ta yanke shawarar goyon bayan tazarcen Buhari ne duba da nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fanoni daban-daban cikin shekaru uku da rabi

- Kungiyar tayi kira da al'umma suyi watsi da wasu da ke kokarin bata sunan shugaba Muhammadu Buhari domin ba su nufin Najeriya da alheri

Kungiyar addinin musulunci na Jama’atul Izalatul Bidi’a Waikamatus Sunnah, JIBWIS, da ke da mambobi a Najeriya, Chadi, Nijar da Kamaru ta bayyana goyon bayanta ga tazarcen Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Shugaban masu da'awah na kungiyar, Ibrahim Jalo-Jalingo ne ya bayar da wannan sanarwar a wani taron wa'azi da kungiyar tayi a garin Jimeta da ke Yola a ranar Juma'a.

2019: Kungiyar Izala ta umurci mambobinta su zabi Buhari
2019: Kungiyar Izala ta umurci mambobinta su zabi Buhari
Asali: Twitter

An shirya wa'azin ne domin murnar daurin auren 'ya'ya mata guda biyu na shugaban kungiyar na kasa, Sheikh Abdullahi Bala-Lau.

DUBA WANNAN: 'Yan majalisar dokoki 2 sun fita daga APC a Jigawa

Wadanda suka wakilci shugaba Muhammadu Buhari a wurin taron sun hada da babban sakataren gidan gwamnati, Jalal Arabi, hadimin shugaban kasa, Sarki Abba da Garba Shehu da kuma dan uwan shugaba Buhari, Musa Daura.

Ibrahim Jalo-Jalingo ya ce kungiyar ta cimma matsayan goyon bayan Buhari ne saboda nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fanin yaki da rashawa, yaki da 'yan ta'addan Boko Haram, farfado da noma da tattalin arzikin Najeriya.

"Al'umma sunyi na'am da nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu cikin shekaru uku da rabi hakan yasa muka yanke shawarar fadawa mambobin mu su zabi Shugaba Muhammadu Buhari da sauran 'yan takarar da ke aiki tare da shi," inji shi.

A cewar babban malamin, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tana kan alkibla shi yasa kungiyar Izala ke goyon bayan ta.

Malamin ya gargadi al'umma kan wasu bata gari da ke kokarin bata sunan shugaba Muhammadu Buhari inda ya ce makiyan Najeriya ne su.

Sauran manyan mutane da suka hallarci taron sun hada da gwamnonin jihohin Adamawa da Zamfara da kuma mataimakan gwamnonin Bauchi da Taraba da kuma wasu 'yan majalisun tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel