Wa'adi: Ababe 5 da ya kamata ku sani game da Marigayi Sarkin Lafiya

Wa'adi: Ababe 5 da ya kamata ku sani game da Marigayi Sarkin Lafiya

A yau Alhamis, Sarkin Lafiya Alhaji Isa Mustapha Agwai I, ya riga mu gidan gaskiya a wani asibitin koyarwa na kasar Turkiya da ke garin Abuja bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Sarkin Lafiya Alhaji Isa Mustapha Agwai
Sarkin Lafiya Alhaji Isa Mustapha Agwai
Asali: UGC

Marigayi Agwai mai shekaru 89 a duniya ya riga mu gidan gaskiya bayan ya shafe tsawon shekaru 43 a bisa kujerar mulki ta masarautar tsohon garin Lafiya da ta kasance Masarautar jihar Nasarawa baki daya.

A yayin da al'ummar Najeriya musamman na jihar Nasarawa ke ci gaba jimamin wannan babban rashi, jaridar Legit.ng ta kawo muku wasu muhimman ababe da ya kamata ku sani game da marigayi Sarkin Lafiya.

1. Marigayi Sarkin Lafiya ya kasance tsatso na gidan sarautar Sarki Aliyu Ari. An haife shi a ranar 15 ga watan Fabrairu, 1935, a kofar Kaura ta garin Lafiya. Ya kasance ɗa ga Muhammad Almustapha Marafa da kuma mahaifiyar sa Hajiya Halimatu.

2. Ya yi karatun Allo a makarantar koyon Al-Qur’ani mai girma ta kofar Kaura, idan bayan samun ilimin wasu surori daidai gwargwado ya tafi makarantar Firamare a shekarar 1943.

3. Bayan kammala karatun sa na Firamare a shekarar 1951, ya kuma yi karatun sa na Sakandire ta Katsina Ala a shekarar 1958. Daga bisani ya yi karatun Difloma a fannin nazarin lissafin kudi a jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria a shekarar 1959.

KARANTA KUMA: Zan kammala dukkanin ayyuka kafin na sauka daga kujera ta - Gwamnan jihar Legas Ambode

4. Ya rike sarautar Dan Galadima da kuma dagacin garin Obi, inda ya jajirce wajen habaka harkokin kasuwanci da kuma noma.

5. Ya kuma yi amfani da rawanin sa wajen inganta ci gaban babbar kasuwar nan ta Agyaragu da ta kasance cibiyar kasuwanci a garin Obi. Ya habaka harkokin sufuri da kuma ilimi inda ya jajirce wajen assasa makarantar sakandire ta garin Obi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel