Ibtila’I ya auku a jahar Legas, hatsarin jirgi ya rutsa da jama’a da dama

Ibtila’I ya auku a jahar Legas, hatsarin jirgi ya rutsa da jama’a da dama

Wani ibtila’I ya rutsa da mutane da dama yayin da jirgin kasa cike da fasinjoji ya tuntsura daga kan layin dogo a daidai kasuwar dabbobi ta Ashade dake kusa da tashar Magoro, a cikin unguwar Agege ta jahar Legas, kamar yadda Legit.com ta ruwaito.

Wannan mummunan lamari ya faru ne da misalin karfe 7 na safiyar Alhamis 10 ga watan Janairu, sai dai an auna arziki babu wanda ya rasu a sakamakon hadarin, amma akalla mutane bakwai sun samu munanan rauni, wanda a yanzu suna samu kulawa a asibiti.

KU KARANTA: Babban Magana: Buhari ba shi da wata kima, yaki da rashawa karyace – Inji Bukola Saraki

Ibtila’I fa auku a jahar Legas, hatsarin jirgi ya rutsa da jama’a da dama
Jirgin
Asali: UGC

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jahar Legas, LASEMA,Tiamiyu Adesina ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai yace da misalign karfe 7:15 na safiyan Alhamis suka samu labarin hatsarin, inda yace jirgin na makare da fasinja akan hanyarsa ta zuwa Ebute Metta.

Sai dai yace binciken da suka gudanar ya nuna hatsarin ya faru ne a sanadiyyar lalacewar hanya a daidai inda layin dogo ya hadu da titin mota, kuma yace sun dade da janyo hankalin hukumar kula da titunan jihar Legas don gyaran hanyar, amma bata yi ba.

Ibtila’I fa auku a jahar Legas, hatsarin jirgi ya rutsa da jama’a da dama
Jirgin
Asali: UGC

Zuwa lokacin tattara wannan rahoto an hangi jami’an hukumar jirgin kasa na Najeriya, NRC, suna kokarin tayar da taragon jiragin da suka fadi ta hanyar amfani da manyan motoci masu na’urar daukan kaya, haka zalika jami’an Yansanda, kashe gobara, kare haddura da sauransu sun mamaye wajen don gudun ko ta kwana.

Ibtila’I fa auku a jahar Legas, hatsarin jirgi ya rutsa da jama’a da dama
Jirgin
Asali: UGC

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng