Arzikin Dangote ya yi kasa, na Adenuga ya yi sama - Kiyasin Forbes
- Wasu 'yan Najeriya sun koka bayan an bayyana cewar arzikin Aliko Dangote ya yi kasa
- A cikin kwana-kwanan nan ne Forbes ta fitar da jerin attajiran duniya kuma har yanzu Dangote shine na farko a Afirka
- Sai dai arzikinsa ya yi kasa daga $12.4bn a shekarar 2018 zuwa $10.3bn a Janairun shekarar 2019
Attajirin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote ya sake kasancewa mutumin da yafi kowa arziki a nahiyar Afirka karo na takwas a jere duk da cewa wannan karon kudinsa ya ragu da $2 biliyan daga $12.2 biliyan da ya ke dashi a Janairun 2018 zuwa $10 biliyan a Janairun 2019.
Wannan rahoton yana kunshe ne cikin jerin sunayen attajiran duniya da Forbes ta fitar a jiya Laraba 9 ga watan Janairun 2019.
Shugaban kamfanin sadarwa na Globacom, Mike Adenuga wadda ke fadada kasuwancinsa zuwa harkar man fetur da dilancin gidaje ya samu karin arziki a wannan shekarar.
DUBA WANNAN: Sojoji sun kwato manyan bindigu 45 daga hannun 'yan ta'adda a jihar Arewa, hoto
Forbes ta bayyana cewar arzikin Adenuga ya karu daga $5.3 biliyan zuwa $9.2 biliyan.
Kazalika, Shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu shima ya samu shiga cikin jerin attajiran duniya a karo na farko tun shekarar 2015.
Kamfanin simintin Kalambaina ta hade da kamfanin simintin Najeriya na Arewa a disambar 2018. Rabiu ne ke da 97% na hannun jarin kamfanin.
Attajira Folorunsho Alakija 'yar Najeriya itama kudinta ya rage daga $1.3 biliyan zuwa $1.1 biliyan.
Forbes ta ce hauhawan farashin hannun jari da faduwar darajan kudaden kasashe yana daga cikin dalilan da yasa adadin biloniyoyin nahiyar Afrika suka rage da 23 a bara zuwa 20 a bana.
A jerin attajiran na kasashen Afirka, Egypt da Afirka ta Kudu suna da biloniyoyi biyar kowannensu, sai Najeriya ke biye da su da biloniyoyi hudu sai Morocco na da guda biyu. Angola da Algeria da Tanzania da Zimbabwe suna da biloniyoyi daya a kasashensu.
Yan Najeriya da damu sun nuna damuwarsu a shafukan sada zumunta inda suka ce rashin kyakyawan yanayi a kasar ne ya janyo arzikin Dangote ya yi kasa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng