Siyasar Kano; Ganduje ya rantsar da sababbin kwamishinoni guda 4

Siyasar Kano; Ganduje ya rantsar da sababbin kwamishinoni guda 4

Daga karshe dai gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da sababbin kwamishinoni guda hudu bayan cika duk wata sharudda da kundin tsarin mulki ya gindaya, musamman ma tantancewar majalisar dokokin jahar.

Legit.com ta ruwaito sabbin kwamishinonin sun hada da Dakta Muhammad Tahir Adamu, Alhaji Mukhtar Ishaq Yakasai, Alhaji Shehu Muhammad Na’Allah, da kuma Injiniya Bashir Yahaya Karaye.

KU KARANTA: Ban cire rai ba, zan cigaba da masa addu’ar shiriyar Allah – Inji Mahaifin wani dan Boko Haram

Siyasar Kano; Ganduje ya rantsar da sababbin kwamishinoni guda 4

Ganduje
Source: Facebook

Ganduje ya rantsar da sabbin kwamishinonin ne a ranar Laraba 9 ga watan Janairu a fadar gwamnatin jahar Kano, inda yayi kira a garesu dasu kasance masu nuna hazaka, gaskiya da amana a yayin sauke nauyin da aka daura musu.

Kwamishina shari’a, kuma babban lauyan jahar Kano, Barista Ibrahim Mukhtar ne ya gabatar da rantsuwar kama aiki ga dukkanin kwamishinonin, inda suka rantse dauke da littafi mai tsarki Al-Qur’ani da kundin tsarin mulkin kasa.

Da yake nasa jawabin jim kadan bayan kwamishinonin sun karbi rantsuwar fara aiki, Ganduje ya bayyana ma’aikatan da ya tura kowanne daga cikinsu, inda yace Dakta Adamu shi zai kula da ma’aikatar ilimin gaba da sakandari, Mukhtar Yakasai kuma kwamishinan ayyuka na musamman.

Siyasar Kano; Ganduje ya rantsar da sababbin kwamishinoni guda 4

Jama'a
Source: Facebook

Sauran kwamishinonin sun hada da Muhammad Na-Allah da aka nada shi kwamishinan tsare tsare da kasafin kudi, sai kuma Injiniya Bashir Karaye a matsayin sabon kwamishinan kimiyya da fasaha da kuma kirkire kirkire.

Ganduje ya bayyana a yayin taron cewa sun mayar da tsohon kwamishinan kasafin kudi zuwa ma’aikatan ilimi, sa’annan yayi kira garesu da su ji tsoron Allah a yayin da suke gudanar da ayyukansu, kuma su kasance masu tsantseni da gaskiya.

Siyasar Kano; Ganduje ya rantsar da sababbin kwamishinoni guda 4

Ganduje
Source: UGC

“Ina da tabbacin kwamishinonin nan ba zasu bani kunya ba, kuma ba zasu kunyata jama’an jahar Kano ba, ina kira ga jama’an jahar Kano dasu basu goyon baya, domin kuwa sune zasu taimaka mani wajen magance matsalolin da suka dabaibaye jahar Kano.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel