Boko Haram sun bawa garuruwa biyu a Borno wa'adi

Boko Haram sun bawa garuruwa biyu a Borno wa'adi

An zargi mayakan kungiyar Boko Haram da bawa mazauna garuruwan Jakana da Mainok wa'adin barin gidajensu ko su kashe su.

Majiyar legit.ng ta rawaito cewar wasu mazauna garin Jakana sun shaida masu cewar mayakan Boko Haram sun basu wa'adin barin gidajensu a yau, Laraba, ko kuma su kashe su.

"Bayan harin da suka kai garin Aunu, mayakan kungiyar sun aiko mana sakon cewar kar mu wuce ranar Laraba (yau) bamu bar garinmu ba," daya daga mazauna garin ya shaidawa majiyar mu.

Sai dai wata majiya daga cikin jami'an tsaro ta ce dakarun soji da hadin gwuiwar jami'an tsaro na musamman na gudanar da bincike na gida-gida a garuruwan biyu dake karamar hukumar Kaga.

An fara binciken ne tun duku-dukun safiya kuma babu tabbacin an kammala shi ya zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto.

Boko Haram sun bawa garuruwa biyu a Borno wa'adi

Wasu mutane da sjoji suka kubutar da hannun 'yan Boko Haram
Source: Facebook

"Muna aiki bisa bayanan da muka samu domin kare rayukan jama'a", a cewar majiyar jami'an tsaro.

Tuni dai rundunar soji ta karyata rahoton dake yawo a gari cewar ta datse hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Ko a ranar Litinin sai da Legit.ng ta kawo maku labarin cewar matasan yankin da suka bad garuruwan zuwa Monguno don neman tsira suka sanar da hakan.

DUBA WANNAN: Tsaro: Rundunar soji ta mika mutane 71 ga rundunar 'yan sanda a Adamawa, hoto

Domin bawa irin wadannan matasa da jama'ar garuruwan da abun ya shafa, gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya kwana guda a garin Monguno yayin hutun karshen mako.

Dakarun soji sun yi nasarar dakile harin da mayakan Boko Haram suka kai a yunkurin su na son kama garin Monguno a satin da ya gabata.

Sai dai duk da mayakan na Boko Haram basu samu nasara ba, mutane da dama dake garin na Monguno sun gudu zuwa Maiduguri domin samun kwanciyar hankali, amma ziyarar gwamnan ta saka da dama sun koma gidajensu kuma cigaba da harkokin rayuwa na yau da gobe.

Sai dai har yanzu mayakan Boko Haram na cigaba da kira ga matasan garuruwan Baga, Doron Baga da sauransu da su shiga kungiyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel