Idan har akwai wanda ya san wata barna da Iyali na su kayi, to ya bankado ta – Buhari

Idan har akwai wanda ya san wata barna da Iyali na su kayi, to ya bankado ta – Buhari

A shekaran jiya ne shugaban kasa yayi wata hira da gidan talabijin nan na Arise TV inda ya kare wasu matakai da gwamnatin sa ta dauka musamman a bangaren tsaro da kuma yaki da rashin gaskiya.

Idan har akwai wanda ya san wata barna da Iyali na su kayi ya bankado – Buhari

Buhari ya nemi a tonawa Yusuf Buhari ko Aisha Buhari asiri
Source: Facebook

Shugaban kasar ya musanya cewa gwamnatin sa tana daurewa wasu manyan barayin kasa gindi a Najeriya. Shugaba Buhari ya nuna cewa ba da ‘yan adawa kurum yake yaki ba idan har aka zo kan batun yaki da sata da barna.

Buhari ya kalubalanci jama’a su fallasa na-kusa da shi, daga Mai dakin sa, Aisha Buhari har zuwa ‘Ya ‘yan sa. Shugaban kasar ya fadawa ‘yan jarida su bankado wani rashin gaskiya da Iyalan na sa su kayi da jami’an gwamnati.

KU KARANTA: Ta tabbata Shugaban kasa Buhari bai da hannun jari a Keystone

Shugaba Buhari ya bayyana cewa bai taba cewa hukumar EFCC ko ICPC da ke yaki da rashin gaskiya su daina gudanar da bincike a kan wani ba. Buhari ya nuna cewa fadar hakan, yunkuri ne na a bata masa suna da kuma kima.

A tattaunawar, shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa yana bi sannu a tsanake wajen yaki da rashin gaskiya ne tun bayan da aka hambarar da gwamnatin sojan sa a 1985.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel