Zabe: Alkalin alkalai na kasa ya aika sako na musamman ga dukkan alkalan kasar nan

Zabe: Alkalin alkalai na kasa ya aika sako na musamman ga dukkan alkalan kasar nan

Walter Onnoghen, alkalin alkalai na kasa, ya bukaci alkalan kasar nan da su kasance cikin shiri a kan korafe-korafen da zasu biyo bayan zabukan shekarar nan da za a yi a cikin watan Fabrairu.

Onnoghen na wannan kalamai ne a jiya, Talata, yayin rantsar da Uwani Abba Aji a matsayin babbar alkaliya ta kotun koli.

Uwani ta kasance mace ta bakwai da ta taba rike wannan mukami.

Alkalin alkalan ya yi fadakar wa mai ratsa jiki ga ma'aikatan bangaren shari'a dasu zama masu bin doka da tsarin aiki wajen sauke nauyin hakkin dake wuyansu.

A cewar Onnoghen, "dole a matsayinmu na ma'aikatan shari'a mu yanke hukunci bisa adalci, yin hakan ne kadai zai tabbatar da dorewar dimokradiyya."

Zabe: Alkalin alkalai na kasa ya aika sako na musamman ga dukkan alkalan kasar nan

Jastis Walter Onnoghen
Source: Depositphotos

Da yake taya Uwani murnar samun sabon mukamin da ya rantsar da ita a kai, Onnoghen ya yi kira gare ta data zama mai biyayya ga rantsuwar da ta yi domin kare mutuncin bangaren shari'a.

DUBA WANNAN: Sayen katin zabe asarar kudi da bata lokaci ne - INEC

A shekarar 2005 ne Maryam Aloma Mukhtar ta zama mace ta farko da aka taba bawa shugabancin kotun koli ta kasa kafin daga bisani ta rike mukamin alkalin alkalai na kasa.

Ragowar mata da suka rike mukamin kafin nadin Uwani sune; Jastis Olufunlola Adekeye, Jastis Mary Peter Odili, Clara Bata Ogunbiyi, Kudirat Keke-Ekun da Amina Adamu Augie.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel