2019: Sakataren jam'iyyar PDP na jihar Kebbi ya koma APC

2019: Sakataren jam'iyyar PDP na jihar Kebbi ya koma APC

Sakataren jam'iyyar PDP reshen jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu Sakaba ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tare da dimbin magoya bayansa.

Sakaba, wanda gwamnan jihar Atiku Bagudu ya tarba ya sanar da ficewars daga PDP ne a ranar Laraba a Birnin Kebbi kamar yadda muka samu daga Daily Trust.

2019: Sakataren PDP na jihar kebbi ya koma APC

2019: Sakataren PDP na jihar kebbi ya koma APC
Source: Twitter

"Na fice daga PDP na koma APC ne saboda nayi imanin cewa Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Atiku Bagudu sun cancanta su jagori 'yan Najeriya."

"Sun mayar da hankali wajen kawo cigabar kasarmu Najeriya da jihar mu a cikin shekaru hudu da sukayi a karagar mulki.

"Fata na shine in tallafa musu domin su cigaba da ayyukan alherin du suka fara shimfidawa al'umma," inji shi.

DUBA WANNAN: Boko Haram sun sake tafka wani sabon ta'addanci a Borno

Sakaba ya yi alkawarin tattaro dubban magoya bayansa domin su jefa wa Buhari da Bagudu kuri'a a babban zaben 2019 da ke tafe.

"Zamu taimaka musu domin ganin Najeriya ta koma dogaro ga noma a maimakon man fetur a matsayin hanyar samun kudaden shiga," inji shi.

A jawabinsa, Bagudu ya yabawa Sakaba bisa goyon bayan da ya ke bawa gwamnatin jam'iyar APC a karkashin shugaba Buhari.

Gwamnan ya yi kira ga dukkan al'ummar jihar masu kishin jihar suyi koyi da Sakaba wajen ganin jihar ta cigaba kamar yadda NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel