Ban cire rai ba, zan cigaba da masa addu’ar shiriyar Allah – Inji Mahaifin wani dan Boko Haram

Ban cire rai ba, zan cigaba da masa addu’ar shiriyar Allah – Inji Mahaifin wani dan Boko Haram

Wani dattijo dan shekara tamanin a rayuwa, Malam Baba Modu ya yi ka dansa mai suna ‘Ba-Ana’ wanda a yanzu haka yana daya daga cikin kwamandojin yaki na kungiyar ta’addanci ta Boko Haram da ya mika wuya ga hukuma, ya rungumi zaman lafiya.

Baba Modu ya bayyana haka ne cikin wata zantawa da yayi da wakilin kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, a ranar Laraba 9 ga watan Janairu a garin Maidugurin jahar Borno, inda yace duk kokarin da yayi na jan hankalin dansa ya ci tura.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Yan bindiga da sun yi garkuwa da wata kansila Mace a Katsina

Majiyar Legit.com ta ruwaito Baba Modu yaso yayi amfani da damar da gwamnatin tarayya ta baiwa mayakan Boko Haram na neman afuwa da yafiya idan har suka mika kansu ga Sojoji tare da ajiye makamansu, amma yace Ba-Ana ya ki yarda.

Ban cire rai ba, zan cigaba da masa addu’ar shiriyar Allah – Inji Mahaifin wani dan Boko Haram

Baba Modu
Source: UGC

Dattijon yace a shekarar 2012 ne mayakan Boko Haram suka shigar da Ba-Ana cikin kungiyarsu a wata gona dake cikin karamar hukumar Dikwa ta jahar Borno. “Da fari na cire ran sake ganin Dana tun bayan shekaru bakwai da suka daukeshi, amma wata rana na hadu da wani mutumi daya bayyana min cewa dana na raye, sa’annan ya bayyana min inda zan sameshi.

“Mutumin ya fada min cewa Ba-Ana ya zama kwamandan yaki a Boko Haram amma bangaren Abu Mus’ab Al-barnawi, wata rana na kama hanya har zuwa yankin tafkin Chadi don shawo kan Ba-Ana, na kwashe sati guda kafin na kai ga inda yake.

“Da isata sansaninsu sai na fada musu nine mahaifin Ba-Ana, daga nan suka fara min tambayoyi domin su tabbatar da gaskiyata ko akasin haka, sai suka ce na jirashi ya dawo daga wani aiki da suka turashi. Sai cikin dare Ba-Ana ya dawo, kuma ya tabbatar musu ni mahaifinsa ne.

“Na kusan kwanaki 30 ina rokonsa ya fita daga Boko Haram ya dawo gida, amma yaki amincewa da shawarana, kuma ya tabbatar min da cewa ya kashe mutane da dama, sa’annan yace yana ganin gwamnati ba zata yafe masa laifukan daya aikata ba, amma yace ya san aikin Allah yake yi.” Inji shi.

Sai dai abinka da soyayyar dake tsakanin Uba da da, Baba Modu yace ba zai hakura ba, kuma bai cire rai akan dansa ba, domin kuwa har yanzu yana yi masa addu’ar Allah ya shiryeshi Ya kuma dawo musu dashi gida.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel