Sha’awa ta jefa wani mutum ga matsala bayan ya zakke ma matar makwabcinsa a Katsina

Sha’awa ta jefa wani mutum ga matsala bayan ya zakke ma matar makwabcinsa a Katsina

Da ake yi ma Katsinawa kirarin kunya kuke baku da tsoro, an samu wani mutumi mara tarbiyya da ya musanta wannan kirari, inda aka kamashi yana zakke ma matar makwabcinsa ta hanyar yi mata fyade da karfi da yaji, inji rahoton Punch.

Majiyar Legit.com ta ruwaito jami’an rundunar Yansandan jahar Katsina sun samu nasarar cafke wani mutumi mai suna Imrana Haruna dan shekara 25 bayan sun samu rahoton yayi ma wata matar aure fyade da suke zama a gida daya.

KU KARANTA; Shugaban kasa Buhari ya sanya labule da El-Rufai a fadar Villa

Mijin wannan mata, Musa Idris ne ya kai shigar da kara zuwa ofishin Yansanda na karamar hukumar Kafur, wanda ta kai ga Yansanda suka kama wanda ake zargi da tafka wannan laifi, daga bisani kuma aka gurfanar da shi gaban kotu.

Dansanda mai shigar da kara ya bayyana ma kotun majistri dake zamanta a cikin garin Katsina cewa lamarin ya faru ne a kauyen Bayala na karamar hukumar Kafur ta jahar Katsina a ranar 22 ga watan Satumbar shekarar 2018.

Dansanda yace makwabtan suna zama ne a gida daya, inda a wannan rana Haruna ya kutsa kai cikin dakin matar ba tare da izini ba, kuma yayi mata fyade, a lokacin mijinta Malam Musa ya fita daga gida.

Da wannan ne dansanda mai shigar da kara, Sajan Lawal Bello ya shaida ma kotu cewa laifin da ake tuhumar Haruna da aikatawa ya saba ma sashi na 348, 262 da 283 na kundin dokokin hukunta manyan laifuka na jahar Katsina.

Sai dai Dansandan ya nemi kotu ta dage sauraron kara saboda har zuwa yanzu basu kammala gudanar da bincike akan lamarin ba, daga nan Alkalin kotun, Fadilo Dikko ta amince da bukatar Dansandan, sa’annan ta bada umarnin a garkame Haruna a gidan kurkuku zuwa ranar 7 ga watan Maris.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel