Shugaban kasa Buhari ya sanya labule da El-Rufai a fadar Villa (Hotuna)

Shugaban kasa Buhari ya sanya labule da El-Rufai a fadar Villa (Hotuna)

Guda daga cikin yan gaban goshin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, gwamnan jahar Kaduna ya kai ma shugaban ziyara a gidansa dake fadar gwamnatin Najeriya inda suka tattauna muhimman batutuwa.

Malam ya kai wannan ziyarar ne a ranar Talata 8 ga watan Janairu, inda aka hangeshi sanye da manyan kaya, yayin da shima Buhari yake sanye da manyan kaya, a wani daki dake nuna lallai ba’a ofis Malam ya samu Buhari ba, a gida ne.

KU KARANTA: Yan dagajin Malamai ne ke janyo mana rikici a Najeriya – Sultan

Shugaban kasa Buhari ya sanya labule da El-Rufai a fadar Villa (Hotuna)

Buhari da El-Rufai
Source: Facebook

Sai dai wani abu daya dauki hankalin jama’a shine yadda Buharin da Malamin gwamnan suka yi irin abin nan da ake ce ma was an yara, inda suka daga tafukan hannayensu suka yi nuni da yatsu hudu a tafin dama, hudu a tafin hagu.

Wannan nuni da shuwagabannin biyu suka yi shine alamar neman tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ke nufin hudu a tara da hudu (4+4), watau takwas kenan, ma’ana suna fata shugaba Buhari zai zarce a karagar mulki, ya kai shekara takwas.

Shugaban kasa Buhari ya sanya labule da El-Rufai a fadar Villa (Hotuna)

Buhari da El-Rufai
Source: Facebook

Idan za’a tuna kundin tsarin mulkin Najeriya ya halasta ma masu rike da mukaman siyasa daga bangaren zartarwa dasu sake tsayawa neman takarar kujerarsu a karo na biyu, matukar jimillan wa’adin da zasu kwashe akan mukaman basu haura shekaru takwasa ba, duba da cewa shekara hudu ake yi a kowanni zangon mulki.

Shi kuwa a nasa bangaren, El-Rufai bai bayyana dalilin zuwansa fadar shugaban ba, amma masana siyasar Najeriya na ganin baya wuce kan batun zaben 2019 dake karatowa, tunda dai labarin gizo baya wuce na koki, inji Hausawa.

A baya dai gwamnan ya sha fadin yadda tauraruwar Buhari ta taimakeshi, inda yake danganta duk wata nasara daya samu a siyasa ga shaharar da Buhari yayi, wanda shima ya raba har ta kai shi ga zama gwamnan jahar Kaduna bayan ya lallasa gwamna mai ci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel