Rabiu Biyora ya watsar da tafiyar Buhari bayan ya gana da Atiku

Rabiu Biyora ya watsar da tafiyar Buhari bayan ya gana da Atiku

Jiya mu ka tabbatar da cewa Rabiu Biyora, wanda yana cikin manyan Masoyan shugaba Muhammadu Buhari, ya sauya-sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya daf da zaben 2019.

Rabiu Biyora ya watsar da tafiyar Buhari bayan ya gana da Atiku
Rabiu Biyora ya koma PDP bayan wulakanta su da aka yi
Asali: UGC

Rabiu Biyora, wanda yayi kaurin-suna wajen goyon bayan gwamnatin shugaba Buhari da kuma gwamnatin APC, musamman a kafafen yada labarai ya watsar da tafiyar APC inda ya kama layin ‘dan takarar PDP Atiku Abubakar.

Biyora ya fusata da APC ne bayan da Mai dakin shugaban kasa watau Aisha Buhari ta nada kwamitin yakin neman zabe ba tare da sa sunan su ba. Matashin ya koka da cewa an fi ba ‘yan wasan kwaikwayon muhimmanci a kan su.

KU KARANTA: Har su Atiku sun san cewa Buhari mai gaskiya ne – Osinbajo

Tun ba yau ba dai aka saba yin watsi da Rabiu Biyora da sauran masu kokarin kare gwamnatin Buhari a kafofin sadarwa na zamani. Wannna ya sa wani yaron Atiku ya tako tun daga kasar Faransa domin ya jawo hankalin Matashin.

Muhammad Atiku Abubakar wanda yana cikin ‘ya yan ‘dan takarar PDP, yayi nasarar janyo Rabiy Biyora cikin jirgin yakin na Atiku Abubakar. Yanzu haka Biyora ya dawo PDP har ya gana da Atiku bayan ya saki layin shugaba Buhari.

Jiya kuma kun ji cewa wani tsohon Mai goyon bayan Shugaba Buhari a da ya koma bangaren Atiku Abubakar bayan an nada sa Jagoran Matasan da za su yi wa PDP kamfe a Yankin Neja-Delta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: