Yadda wasu yan mata suka halaka mahaifiyarsu ta amfani da wuka da bindiga

Yadda wasu yan mata suka halaka mahaifiyarsu ta amfani da wuka da bindiga

Wasu yan mata biyu yan gida daya da suka hada da Amariyona Hall mai shekara 14 da kanwarta mai shekaru 12 da ba’a bayyana sunanta ba sun hada kai wajen halaka mahafiyarsu, Erica Hall ta hanyar amfani da wuka da bindiga a ranar Juma’a 4 ga watan Janairu.

Wannan lamari ya faru ne a gidansu dake unguwar Magnolia a jahar Mississippi na kasar Amurka, inda yan matan suka caccaka ma mahafiyarsu wuka a duk jikinta, sa’annan suka dirka mata harsashi a kirjinta, wanda yayi sanadiyyar cikawarta.

KU KARANTA: Yan dagajin Malamai ne ke janyo mana rikici a Najeriya – Sultan

Yadda wasu yan mata suka halaka mahaifiyarsu ta amfani da wuka da bindiga
Erica da Amariyona
Asali: Facebook

Legit.com ta ruwaito da fari yaran sun yi kokarin bi ta kan mahaifiyarsu a cikin wata motar da suke tukawa, toh amma basu samu nasara ba, wannan ne ya harzuka mahaifiyar tasu inda ya ladabtar dasu, a washegari kuma aka tsinci gawarta a kofar gida.

Makwabtan uwargida Erica sun bayyana cewa tana da yaya guda hudu, amma wadannan biyun ne ke bata matsala. Duk kokarin da jami’an hukumar bada agajin gaggawa suka yin a ceto Erica ya ci tura, sakamakon tayi asaran jini dayawa.

Shugaban Yansandan yankin Pike, Kenny Cotton ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace sun samu nasarar kama yan matan da ake zargi su duka, kuma hukuma na tuhumarsu da aikata laifin kisan kai, sa’annan zata mikasu zuwa asibiti domin a duba lafiya kwakwalwarsu.

“In banda abinta, tun lokacin da yaran suka yi kokarin taketa da mota ya kamata ta kai kara domin a kamasu, da duk ba’a kai ga haka ba.” Inji Dansandan Pike.

Haka zalika makwabta sun tabbatar da cewar rikicin ya samo asali ne tun bayan da uwargida Erica ta dauke wayoyin salulan yan matan biyu ne, sai dai Yansanda sun ce basu ga dalilin kasha mahaifiyar tasu da suka yi ba, idan dai akan haka ne.

Amma da ake zantawa da kanwar Erica, Robin Coney, tace yan matan sun bayyana mata cewa basu suka kashe uwarsu ba, amma koda da ta tambayesu suna ina ne a lokacin da aka kashe matar sai suka gagara bata amsa.

“Bayan sun kasheta da bindigarta sai suka fita zuwa gidan wani makocinsu, inda suka nemi ya rage musu hanya zuwa gidan kakarsu da ta rasu a kwanakin baya, amma sai ya ki, yace ba zai kaisu ba har sai ya kira babarsu don ta san inda za su je, daga nan suka yi tafiyarsu, a wannan lokaci ne kanwarsu Ebony ta isa gida ta tarar da gawar mahaifiyarsu a kwance jina jina.” Inji ta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng